✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun karkashe ’yan Boko Haram, sun ceto mata da kananan yara

Sojoji sun yi wa mayakan kungiyar luguden wuta suka kuma kwato mata da kananan yara

Rundunar Sojin Najeriya ta ce dakarunta, yayin ci gaba da aikin kakkabe masu tayar da kayar baya a yankin Arewa maso Gabas, sun kashe mayakan Boko Haram tara a Karamar Hukumar Gwoza ta Jihar Borno.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin ta bakin jami’inta da ke kula da yada labarai, Manjo Janar John Enenche, rundunar ta ce, an kaddamar da samame kan mayakan ne tare da hadin gwiwar dakarun sojin sama da na kasa.

Manjo Janar Enenche ya ce hakan ya biyo bayan samun bayanan sirri da leke da Bataliyar Soji mai lamba 192 ta gudanar a ranar Lahadi, 6 ga wata Satumban 2020.

Ya ce sojoji sun fatattaki ’yan ta’addan inda suka kashe biyar, yayin da wasu suka tsere da raunin harbin bindiga.

Ya kara da cewa dakarun sun kuma samu nasarar kubutar da mutum bakwai da mayakan suka yi garkuwa da su da suka hadar da mata biyu da kananan yara biyar.