✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun kubutar da mata 42, yara 51 da maza 2 a Borno

Rundunar sojojin Najeriya sun kubutar da mata 42 da yara 51 da kuma maza 2 daga hannun mayakan Boko Haram, wadanda suke amfani da su…

Rundunar sojojin Najeriya sun kubutar da mata 42 da yara 51 da kuma maza 2 daga hannun mayakan Boko Haram, wadanda suke amfani da su a matsayin leburori.

Mukaddashin Daraktan hulda da jama’a na sojojin Najeriya Kanal Sagir Musa, ne ya sanar da hakan, rundunar ta kuma dakile harin ‘yan kungiyar uku.

Kanal Sagir Musa, ya ce 24 daga cikin yaran da aka kubutar, jami’an kiwon lafiya na sojojin sun yi masu rigakafin shan inna.