✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun kama wakilin Daily Trust na Maiduguri

Sojojin Najeriya daga runduna ta 7 na sojan kasa sun je sakatariyar Kungiyar ‘yan jaridu ta Najeriya, (NUJ) reshen jihar Borno, inda suka kama wakilin…

Sojojin Najeriya daga runduna ta 7 na sojan kasa sun je sakatariyar Kungiyar ‘yan jaridu ta Najeriya, (NUJ) reshen jihar Borno, inda suka kama wakilin Daily Trust na Maiduguri, Olatunji Omirin cikin ankwa.

Sojojin su uku, biyu cikin kayan gida daya cikin kaki, sun kama Olatunji ne da misalin karfe 4:40 na yamma.

Sun fara zuwa ofishin shiyya na Daily Trust da ke hanyar Baga ne sau biyu, kafin daga baya suka je cibiyar, inda suka kama shi suka tafi da shi.

Idan ba a manta ba, yau shekara daya da kwana 23 ke nan daidai da sojoji suka je ofishin kamfanin na Maiduguri, inda suka kama Editan shiyya na ofishin da wani wakilin Daily Trust din, Ibrahim Sawab.