✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun fatattaki ‘yan bindiga a Zamfara

Sojojin sun kai samame tare da fatattakar maharan da suka yi kokarin shiga jihar.

Dakarun ‘Operation Hadarin Daji’, sun kai samame tare da fatattakar ‘yan bindiga da dama a maboyarsu a Jihar Zamfara.

Babban Kwamandan runduna ta daya ta sojojin Najeriya da ke Gusau, Birgediya Janar Sani Ahmed ne, ya bayyana hakan a ranar Lahadi.

Ya ce dakarun tare da hadin gwiwar wasu jami’an tsaro, sun fatattaki ‘yan bindigar da suka yi sansani a wasu dazuka da ke wajen jihar.

Kwamandan, ya ce dakarun sun kwato muggan makamai daga maboyar ‘yan bindigar bayan sun fatattake su, inda suke tsere zuwa daji da raunin harbin bindiga.

A cewarsa, sun kai samame maboyar ‘yan ta’addan da aka gano a dajin Sunke, Gando, Munhaye da kuma dajin Kuyanbana.

“Runduna ta 1 ta taimaka sosai waje horas da jami’an tsaron sa-kai sama da 4,000 da gwamnatin jihar ta dauka aiki don tabbatar da tsaro.

“Sauran ‘yan uwa abokan aiki da jama’ar gari sun taimaka wajen samar da magunguna da tallafin kayan aiki ga wasu manyan asibitocin Gusau.”

Ya kuma kara da cewa za a bullo da wasu sabbin dabarun yaki don tabbatar da tsaro da kuma kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Jihar Zamfara.