Sojoji sun kona manyan maboyan ’yan bindiga suka kuma damuke wasu daga cikinsu a jihohin Katsina da Zamfara.
Sansanonin da sojojin suka lalata sun hada da na wani hatsabibin dan bindiga mai suna Abu-Radde a Karamar Hukumar Batsari, Jihar Katsina.
Mukaddashin kakakin rundunar Operation Sahel Sanity da ke jihar, Birgediya Benard Onyeuko, ya ce sun kama ’yan bindiga da masu yi musu leken asirin da dakon kaya masu yawa a jihohin biyu.
Ya ce bayan kama wasu ’yan bindiga a garin Danmusa da ke kan hanyar Runka, “Sojoji da ke sintiri a Binji sun kama wani dan bindiga sanye da kayan wani dan sanda mai suna James Oname.
“Binciken da muka gunadanar ya nuna tun shekarar 2015 ’yan bindiga suka kashe Sajan James Oname a Tungar Rakumi ta Karamar Hukumar Maru da ke Jihar Zamfara. Yanzu haka muna bincikar wanda ake zargin”, inji shi.
Ya ce sojojin sun kuma kama wani mai yi wa ’yan bindiga leken asiri da dakon kaya a garin Dodo a jihar Katsina bayan samun bayanan sirri game da motsinsa.
“Matarsa ta yi zargin cewa da karfin tsiya ya aure ta, yayin da maharan da mijinta ke aiki da su ke zargin ta da sanar da jami’an tsaro game da ayyukansu, wanda hakan ya sa yake azabtar da ita.
“An ceto matar aka mika ta ga Gwamnatin Jihar Katsina, shi kuma mijin ana can ana bincikar sa”, inji Janar Onyeuko.
Ya ce Shugaban Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai ya yaba da namijin kokarin da sojojin suka yi a yankin na Arewa maso Yamma.