Mazauna unguwar Hotoron Arewa a Karamar Hukumar Nassarawa ta jihar Kano sun shiga halin firgici a ranar Asabar bayan da dakarun sojoji suka kai samame wani sabon gida tare da kame mazauna cikinsa da ake zargin ’yan ta’adda ne.
Rahotanni dai sun ce sojojin sun yi dirar mikiya ne a gidan wanda yake Filin Lazio a yankin da misalin karfe 9:15 na daren ranar Asabar.
- ’Yan IPOB sun kai hari ofishin ’yan sanda a Akwa Ibom, sun kashe mutum 6
- Karuwanci: An ceto ’yan mata 22 da aka killace a otal a Ogun
A cewar wani mazaunin yankin, Malam Muhammad Amadi, sojojin sun yi awon gaba da ilahirin mutanen da suka tarar a gidan.
Ya ce ba a sami tirjiya ko kadan ba daga mutanen yayin kamun, kuma ba a harba ko da harsashi daya ba a samamen da aka shafe kimanin mintuna 30 ana yi.
Wani mazaunin yankin ya shaidawa Aminiya cewa tun a baya dama mutanen unguwar sun jima suna dari-dari da gidan, kasancewar ya kasance wata matattara ga ’yan gudun hijira daga Arewa maso Gabas, musamman jihar Borno a ’yan kwanakin nan.
A cewar majiya, “Yanayin irin facakar da mutanen suke yi da kuma yadda suka kebance kansu ya jefa alamar tambaya a zukatan mutanen anguwar da dama, kuma ina kyautata zaton wannan ma shine makasudin wannan kamen.
“Na ji wasu na jita-jitar cewa wai a masallaci aka kama su, amma ba gaskiya ba ne, a cikin gidan aka kama su,” inji majiyar.
Kakakin Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya a Kano, Kaftin Njoko Irabor ya tabbatarwa da Aminiya kamen.
Ya ce sun sami kama mutanen ne sakamakon wasu bayanan sirri da suka samu a cikin irin kokarin da suke yi na raba jihar da bata-garin dake son amfani da zaman lafiyan dake garin wajen tayar da zaune tsaye.