✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sojin Isra’ila sun kashe Falasdinawa 4, sun jikkata sama da 40

Rahotanni sun ce Falasdinawa hudu ne aka kashe, wasu fiye da 40 kuma suka jikkata a wani samame da sojojin Isra’ila suka kai a sansanin…

Rahotanni sun ce Falasdinawa hudu ne aka kashe, wasu fiye da 40 kuma suka jikkata a wani samame da sojojin Isra’ila suka kai a sansanin ‘yan gudun hijira da ke Jenin a Arewa da gabar kogin Jordan.

Yayin samamen, gomman motocin yakin sojin Isra’ila aka gani sun yi jerin-gwano zuwa cikin sansanin da misalin karfe 9:00 na safe daidai da karfe 06:00 a agogon GMT.

Ma’aikatar Lafiya ta Falasdinu ta sanar a safiyar Laraba cewa, mutum hudun da aka kashe su ne Ahmad Alawneh da Abed Hazem da Mohammad al-Wanneh da kuma Mohammad Abu Naa’sah wanda baki dayansu matasa ne ‘yan tsakanin shekara 26 zuwa 30.

Gidan talabijin na Al-Jazeera ya rawaito cewa uku daka cikin wadanda aka kashe din ‘yan bindigar Falasdinu ne.

Bayanai sun nuna akalla mutum 44 ne suka jikkata yayin harin.

Sojojin na Isra’ila sun ce sun harbe wasu mutum biyu har lahira wadanda ake zargin suna da hannu a wasu hare-haren da aka kai a baya-bayan nan.