✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Soja ya harbe sojoji 4 sannan ya kashe kansa a Borno

Wani sojan Najeriya mai mukamin kofur da ke aiki da rundunar Operation Lafiya Dole a Jihar Borno, ya harbe abokan aikinsa sojin Najeriya 4, sannan…

Wani sojan Najeriya mai mukamin kofur da ke aiki da rundunar Operation Lafiya Dole a Jihar Borno, ya harbe abokan aikinsa sojin Najeriya 4, sannan ya kuma raunata karin wasu biyu kafin daga bisani ya harbe kansa.

Mai magana da yawun rundunar sojin Najeriya Konel Sagir Musa, ne ya tabbatar da faruwar lamarin ranar Laraba.

Ya ce da sanyi safiyar yau Laraba ne sojan mai mukamin kofur da ke aiki da rundunar Operation Lafiya Dole da ke Malamfatori a jihar Borno, ya budewa abokan aikinsa 4 wuta wadanda suka mutu nan take ya kuma jikkata karin wasu biyu wuta kafin daga bisani ya harbe kansa, ya ce ana bincike domin gano musababbin lamarin.