Shugaban kungiyar ’yan China mazauna Jihar Kano ya yi wa Sarkin Kano Aminu Ado Bayero ta’aziyar matashiyar nan da ake zargin wani dan kasar China da kisanta, Ummukulsum Sani Buhari wadda aka fi sani da Ummita.
Shugaban wanda ya ke tare da wani hadiminsa sun kai ziyara Fadar Sarkin ne a ranar Talata.
- ‘Dan Chinan da ya kashe Ummita ya karbi addinin Musulunci’
- NAJERIYA A YAU: Yanka 11 Na Gani A Jikin Ummita —Mai Wankan Gawa
Kamar yadda Ikrimatu Suleiman wanda ya shaida wa Aminiya ziyarar ta hanyar hoto da sauti, ya ce an yi wa shugaban da dan rakiyarsa iso har gaban sarki.
A cewarsa, da isarsu suka fadi suka yi gaisuwa, sannan shugaban ya umarci dan rakiyar tasa mai suna Tanko da ya karanta takardar jawabin nasa, wanda kuma ya yi da Harshen Hausa.
A jawabin nasa, shugaban ya jajanta wa Sarki, da ‘yan uwa, da iyayen Ummita, sannan ya jaddada goyon bayansa ga matakin hukuncin da ya kama a yi masa.
Sannan ya ambato cewa suna zaune a Kano lafiya tare da gudanar da kasuwancinsu cikin kwanciyar hankali.
Kafin zuwansu gaban sarkin Kano, shugaban ‘yan Chinan ya fitar sanarwar nesanta kansu daga abin da dan kasar ta su ya aika na kisan gilla tare da kira ga hukuma ta dau matakin da ya dace.
Rabi’a N. Garba, aminiyar Ummita da Mista Geng Quanrong ya kashe a Jihar Kano, ta yi karin haske dangane da alakar mutanen biyu da lamarin ya shafa.
A wata zantawa ta musamman da ta yi da Aminiya, Rabi’a N. Garba, ta ce sai da Mista Geng ya karbi addinin Islama sannan marigayiya Ummita ta amince ta fara soyayya shi da zummar za su yi aure.
A halin yanzu dai Mista Geng yana ci gaba da bai wa diddigensa hutu a hannun jami’an tsaro da tuni suka yi ram da shi.
Bayanai sun ce, ’yan unguwa ne dai suka rike dan Chinar tare da mika shi ga jami’an tsaro bayan ya kashe matashiyar mai shekara 23 a gidan iyayenta a ranar Juma’ar makon jiya.
Rahotanni sun bayyana cewa, marigayiya Ummita dai bazawara ce wadda suka rika shan soyayya da dan Chinar tun kafin aurenta, kuma alakar ta ci gaba har bayan ta shiga gidan miji, lamarin da ake zargi shi ya yi sanadiyar mutuwar aurenta.