✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban Ukraine ya kori manyan Hafsoshin tsaron kasar 2 saboda ‘hadin baki’ da Rasha

An dakatar da su har zuwa lokacin da za a kammala bincike

Shugaban Kasar Ukraine, Volodymyr Zelenskyy ya dakatar da Shugaban Hukumar Tsaron Cikin Gida ta Kasar da kuma Babban Mai Shigar da Kara har bisa zarginsu da hannu wajen tallafa wa Rasha.

Dakatarwar za ta ci gaba ne har zuwa lokacin da za a kammala bincike a kansu, kamar yadda wani mataimakin Zelenskyy na musamman ya bayyana.

A ranar Lahadi ce dai Shugaban Kasar ya ce an tsige Ivan Bakanov daga matsayinsa na Shugaban Hukumar Tsaron Cikin Gida ta Kasar , da kuma takwararsa mai gabatar da kara Iryna Venediktova, bisa kama su da laifin hada kai da wasu hukumomi da jami’an Rasha.

Andriy Smyrnov, Mataimakin Shugaban Kasar na musamman ya sanar da gidan Talabijin din Ukraine a ranar Litinin cewa, dakatarwar ta dan wani lokaci ne kafin su kammala bincike.

Da ya ke amsa tambaya a kan ko jami’an biyu za su iya komawa bakin aikinsu idan binciken ya wanke su, sai ya ce a matsayinsu na masu bin dokar kasar, a shirye suke su amince da sakamakon binciken.

Kazalika gidan talabijin na Aljazeeran ya rawaito cewa ana ci gaba da bincike kan jami’an biyu, kuma idan aka samu kwararan hujjoji kan zarge-zargen a kansu, Zelenskyy zai bukaci Majalisar Dokokin kasar da ta tube su daga mukamansu.

“Hukunci irin wannan abin mamaki ne, kasancewar ko a baya Zelenskyy ya yi canje-canje irin su, amma tun lokacin da yakin kasar da Rasha ya fara ya ci gaba da kasancewa da manyan jami’an da ke kewaye da shi ciki har da wadannan manyan mutanen biyu,” inji wakilin Aljazeeran.

A ranar Lahadin da ta gabata ce aka wallafa umarnin dakatar da Bakanov, wanda a da abokin Zelenskyy ne na kuruciya, da kuma Venediktova, wacce ta jagoranci yunkurin gurfanar da laifuffukan yakin Rasha a Ukraine, a shafin yanar gizon Shugaban Kasar.

A wani rubuta da ya wallafa a shafin Telegram, Zelensky ya ce tuni aka fara shari’o’i kan cin amanar kasa guda 651 da jami’an gabatar da kara, da na bangaren masu tabbatar da doka, kuma an gano fiye da jami’a 60 daga hukumomin Bakanov da Venediktova suna aiki da Ukraine a yankunan da Rasha ta mamaye.

Zelenskyy ya ce “Irin wadannan laifuffukan da suka shafi jigon tsaron kasa dole su haifar da tambayoyi ga wadanda ke jagoranta sashen.