Shugaban kasar Malawi, Lazarus Chakwera ya saba alkawarin da ya yi a gangamin yakin neman zabe na samar wa mutum miliyan daya aiki, inda ya ce gwamnati mutum dubu 200 kawai za ta iya dauka.
Shugaba Chakwera ya ce gwamnati ba za ta iya samar da aiki ita kadai ba, sai da taimakon kamfanoni masu zaman kansu.
- Za a debi mutum 7,500 aikin dan sanda a jihar Zamfara
- Buhari ya yi wa malamai karin albashi da shekarun aiki
Ya ce kowanne dan kasuwa akwai bukatar ya kara yawan ma’aikatansa. Shugaban ya shaida hakan ne a jawabinsa na cika kwana 100 kan karagar mulki ranar Litinin da ta gabata.
Samar da aiki miliyan guda shi ne makamin da Jam’iyyarsa ta yi amfani da shi wajen yakin neman zabe.
A rahoton da BBC ta wallafa, masu suka sun shaida wa kafofin yada labaran cikin gida cewa jam’iyyar ba ta da tsarin iya samar da ayyuka, kawai ta yi amfani da wannan batu a matsayin dabarun samun nasarar zabe.