Shugaban Kwalejin Ilimi ta Tarayya dake Zariya (FCE) a jihar Kaduna, Dakta Ango A. Ladan ya rasu.
Rahotanni sun ce ya rasu ne da misalin karfe 3:00 na daren ranar Litinin a gidansa dake Zariya.
- ‘Rikicin Boko Haram ya hallaka mutane 35,000, ya raba 2m sa muhallansu a Borno’
- Sojoji sun fatattaki ’yan Boko Haram daga hanyar Damaturu zuwa Maiduguri
Rajistaran makarantar, Dakta Jibril Lawal ne ya tabbatar da rasuwar a wane rubutaccen sako, inda ya ce za a gudanar da jana’izar mamacin da misalin karfe 2:30 na ranar Litinin a gidansa dake Unguwan Juma a cikin birnin Zariya.
Wa’adin farko na mulkin shugaban dai ya kare ne ranar hudu ga watan Fabrairun 2021.
Sai dai tun lokacin, Gwamnatin Tarayya ba ta sabunta masa wani sabon wa’adin ba kuma ba ta nada wani ba domin maye gurbinsa a hukumance.
Lamarin dai ya yi ta jawo hankulan mutane a makarantar, ko da yake Mataimakin Shugaban Makarantar, Dakta Suleiman Balarabe ne yanzu haka yake tafiyar da jagorancinta.