✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban Koriya ta Arewa zai gana da takwaransa na Kudu

A yau ne shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un zai gana da takwaransa na kasar Koriya ta Kudu Moon Jae-in a wani taro da zai…

A yau ne shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un zai gana da takwaransa na kasar Koriya ta Kudu Moon Jae-in a wani taro da zai gudana a kauyen Panmunjom da ke tsakanin kasashen guda biyu.

Wannan ne karo na biyu da shugabannin kasashen guda biyu za su gana da juna a tarihin kasashen, wanda hakan ke nuni da cewa ana samun ci gaba da harkar zamantakewa da ke tsakanin kashashen biyu.

Manyan jami’an kasashen guda biyu sun gana tun a karshen makon jiya domin shirya wannan taron na kara wa juna sani tsakanin kasashen guda biyu makwabtan juna, bayan kuma kwanakin baya shugaban na Koriya ta Arewa ya zai ziyara kasar Chana, wanda a kai ta yin mamaki.

Hakanan kuma, bayan sun gana, Shugaban kasar Koriya ta Arewa din zai gana da Shugaban kasar Amurka Donald Trump wanda ake tunanin za a yi cikin farkon watan Mayun bana.

A game da taron hadin kai da karawa juna sanin, Shugaban tawagar Pyongyang Rio Son Gwon ya ce an shirya taron ne domin shugabannin kasashen guda biyu su samu damar ganawa da juna .

“A kusan kwana 80 ko sama da haka da suka gabata, wasu abubuwa da suke nuna cewa za a samu damar tattauna alakar da ke tsakanin kasashen Koriya ta Arewa da Koriya ta Kudu sun wakana,” in ji Ri, wanda shi ne shugaban kwamitin sulhu da hadin kai na kasar Koriya ta Arewa.

Farkon abin murna da ya faru a yankin shi ne lokacin da aka fara wasannin Olymfik a Koriya ta Kudu, wanda ya zo kusan shekara daya bayan an ta samun hargitsi da tashin tashina a yankin saboda shirin kasar Koriya ta Arewa na mallakar makamin Nukiliya da sauran makamai masu linzami, wanda ya sa Shugaban Amurka Donald Trump da Shugaban Koriya ta Arewa Kim suka ta kai ruwa rana da cacar baki.

Tun bayan wannan wasannin, an ta samun ci gaba musamman yadda jami’an gwamnatin kasashen suke ta ziryar ziyartar kasashen juna.

Wani mai sharhi a kan al’amuran yau da kullum ya ce samun nasarar wannan taron zai dogara ne kacokan kan shirin ganawa da Kim da Trump ke yi, wanda ba a riga an sa rana ba.

“Idan aka samu ci gaba a shirin tattaunawa tsakanin Amurka da Koriya ta Arewa, wannan zai taimaka matuka wajen samun nasarar taron da za a yi tsakanin kasashen Koriya ta Arewa da Koriya ta Kudu,” in ji Green wanda shi ne babban mai bada shawara ga kungiyar magance rikici a yankin.

Hakanan a nasa bangaren, Farfesa Cheng diaohe na Jami’ar Renmin, a bangaren nazarin harkokin kasashen waje da ke Beijing, idan aka samu nasarar wannan taro, zai taimaka wajen samun cigaba a yankin, “Idan aka yi komai kamar yadda aka tsara, za a biyo bayan taron da wasu tarururruka na jam’iyyu.”

“Babu wanda yake tunanin cewa za a iya magance matsalolin da suka dabaibaye wannan yankin a taro guda daya kawai. Akwai sauran aiki ko da kuwa an yi wannan taron na farko, amma dai ana samun ci gaba sosai a tafiyar.”