✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban Korea ta Kudu ya kafa dokar ta ɓaci don hukunta ƴan adawa

Shugaban Korea ta Kudu Yoon Suk Yeol ya ayyana dokar ta baci, a wani yunƙuri na kare ƙasar daga masu ra’ayin kwamunisanci a daidai lokacin…

Shugaban Korea ta Kudu Yoon Suk Yeol ya ayyana dokar ta ɓaci, a wani yunkuri na kare ƙasar daga masu ra’ayin kwamunisanci a daidai lokacin da ’yan majalisar dokokin ƙasar ke tayar da jijiyoyin wuya kan batun kasafin kuɗi.

A lokacin da yake gabatar da jawabinsa da aka watsa kai-tsaye ta kafar talabijin, shubaban na Korea ta Kudu ya ce, ya ɗauki wannan matakin ne na ayyana dokar soji domin tunkarar barazanar da ke kunno kai daga masu ra’ayin kwamunisancin Korea ta Arewa, dokar da ya ce za ta kawar da irin waɗannan mutanen.

Shugaba Yoon ya ce, jam’iyyar adawa ta kassara harkokin gwamnatin ƙasar ba tare da la’akari da halin da al’umma za su tsunduma a ciki ba, kuma ta yi haka ne saboda matakin da aka ɗauka kan wasu ’ya’yanta da aka tsige su  tare da gudanar da bincike a kansu kan wasu laifuka da suka aikata.

Wannan dambarwar na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyar shugaba Yoon ta People Power Party da jam’iyyar adawa ta Democratic Party ke ci gaba da nuna wa juna yatsa kan kasafin kuɗin baɗi, inda  a makon jiya,  ’yan adawar a majalisar suka amince da zabtare wani gagarumin kaso daga kasafin a karkashin wani kwamitin majalisar, kuma da ma su suke da rinjaye.

Yanzu dai shugaba Yoon ya ce, majalisar tarayyar kasar ta zamo wata mafaka ga miyagu, inda suke yin mulkin kama-karya domin gurgunta ɓangaren shari’a da na gudanarwa a ƙasar.

Shugaban ya kuma zargi ’yan adawar a majalisar da share manyan batutuwan da kasafin ya kunsa na ciyar da ƙasar gaba kamar yaƙi da kwankwadon kwayoyi da kuma inganta tsaron al’umma.

Yan adawar ne dai ke da rinjaye a majalisar dokokin ƙasar mai kujeru 300, yayin da shugaba Yoon ke zargin su da shirya maƙarkashiyar kifar da gwamtainsa.