Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka (CAF) Ahmad Ahmad ya kamu da cutar COVID-19.
Jawabin da CAF ta wallafa a shafinta ya ce “Bayan wasu alamu da shugaban hukumar kwallon kafar Arfika ya nuna, bayan dawowarsa daga kasar Masar ya sa aka yi masa gwaji kuma sakamako ya tabbatar da yana dauke da cutar coroanavirus”.
- Cristiano Ronaldo ya kamu da cutar coronavirus
- Pogba ya kaddamar da asusun tallafa wa masu cutar Kurona
- Dan wasan Manchester United Pogba ya kamu da coronavirus
- An tabbatar da ingancin rigakafin Coronavirus a China
Hukumar ta ce shugaban nata ya killace kansa masaukinsa zuwa tsawon makonni biyu, domin bin dokar da hukumomin lafiya suka tanadar.
Ta kuma yi kira ga dukkanin wanda suka yi mu’amala da shugaban, da su killace kansu kafin gudanar da gwajin kwayar cutar a kansu.