✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban Hukumar Shige da Fice ya kamu da Coronavirus

Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta Najeriya Muhammad Babandede ya kamu da cutar Coronavirus. Muhammad Babandede ya ce a ranar Asabar ne aka…

Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta Najeriya Muhammad Babandede ya kamu da cutar Coronavirus.

Muhammad Babandede ya ce a ranar Asabar ne aka tabbatar ya kamu da cutar.

“Na killace kai na tun bayan da na dawo daga kasar Burtaniya a ranar 22 ga watan Maris inda na biyo jirgin British Airways na sauka a Legas.

“A ranar Lahadi aka tabbatar min cewa, gwajin da aka yi min ya nuna ina dauke da cutar coronavirus”, in ji shi.

Mai magana da yawun hukumar dai ya ce Babandede yana samun kulawa kuma samun sauki.

Hukumomin Najeriya sun tabbatar da cewa zuwa karfe 10.40 na daren Asabar, mutum 97 ne suka kamu da cutar.