Shugaban Amurka Donald Trump ya fada a farkon wannan makon cewa za su dauki matsaya guda shida da takwaransa na kasar Faransa akan batun makamin nukiliyar kasar Iran.
Trump ya yi wannan jawabin ne a lokacin da ya karbi bakuncin takwaransa na kasar Faransa, Emmanuel Macron da uwargidansa Brigitte Macron wanda ya kawo ziyarar aiki kasar Amurka a karon farko tun bayan darewarsa karagar mulki.
Shugaba Trump ya ce wannan matakin ko zai yiwu ba zai wa kasar Iran dadi ba, amma kuma bai bayyana ko zai ci gaba da mutunta yarjejeniyar da aka cimma wa ba da kasar ta Iran.
A wurin liyafar cin abinci da Trump ya shirya wa bakon nasa, ya soki lamirin kasar Iran yana cewa zai tabbatar ya durkusar tare da tsayar da shirin nukiliyar kasar cikin dan kankanin lokaci domin ya gane kasar na Iran na neman tayar da zaune tsaye a yankin kasashen Gabas ta tsakiya.
Trump ya yi kalamai da kakkausar lafuzza a lokacin wannan zaman cin abincin yana cewa muddin kasar Iran ta yi kasassabar ci gaba da sarrafa makamin ta na nukiliya to ta kwana da sanin cewa za ta dandana kudarta, domin wannan zai janyo mata matsala mai girma wanda ba za ta iya dauka ba.
Sai dai dama Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani ya dauki sake yunkurin kakabawa kasarsa takunkumin tamkar janyewa ne daga yarjejeniyar da kasar ta Iran ta cimmawa da manyan kasashen nan shida na duniya, shi ma Rauhani ya yi gargadi ga Amurka da kada ta sake ta ce za ta janye daga wannan batu, domin ba ita kadai ce aka yi matsayar da ita ba.
A cewarsa, muddin dai Amurka ta janye daga cikn wannan yarjejeniyar to ba shakka hakan zai kara tsumduma kasashen na yankin gabas ta tsakiya cikin damuwa.
A waje daya kuma Shugaban Faransa Emanuel Macron ya janyo hankalin kasar ta Iran ne da ta mutunta yarjejeniyar da aka yi da ita yana cewa kada Iran ta ce za ta kara fadada sarrafa makamin nukiliya bayan an cimma matsaya da ita.
Haka kuma Macron ya bukaci Trump da kada ya yi gaggawar fidda sojojin Amurka daga cikin kasar Syria, yana cewa yin hakan tamkar ya mika kasar ce ga mulkin Bashar Al-Assad wanda yake mulkin ta’addanci tare da goyon bayan kasar Iran.
Amma kafin Macron ya kawo wannan batu a lokacin wannan liyafa, sai da Trump ya ce ba laifin kowa bane illa na kasashen da ke yankin kuma suna ganin abinda Syria ke aikatawa amma suka ki su ce komai domin ganin an kori ’yan ta’adda a yankin.
Trump ya ce Amurka ta kashe makuddan kudade a yankin Gabas ta tsakiya har na tsawon shekara 18, amma ba wani abu da za ta nuna ta ce shi ne ta amfana da shi sakamon wadannan kudaden da ta kashe.
Wani masanin harkokin tsaro na kasar Iran mai suna Benham Ben Taliblu ya ce muddin kasar Amurka ta yi rashin dabarar ficewa daga cikin wannan yarjejeniyar, to hakan zai bai wa Iran kafar sarrafa makaminta na Nukiliya domin ko tana da hujja na cewa tunda Amurkar ce ta fice, wannan yana nufin tana iya daukar mataki a kan Iran din wanda kuma Iran ba za ta tsaya sai an dauki mataki akanta ba kafin ta yi abin da take ganin ya dace da makaminta na Nukiliya ba.Taliblu ya ce sai dai Iran za ta yi kokarin ganin sauran kasashen Yammacin Turai da ma sauran kasashen duiniya sun nuna kin goyon bayansu ga ficewar Amurka cikin wannan yarjejeniyar to hakan ne kawai zai sa Iran ta kwantar da hankalin ta game da yarjejeniyar.