✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Shugaban APC ya shiga bayan labule da gwamnonin jam’iyyar

Taron na sirri na gudana a shelkwatar jam’iyyar da ke Abuja.

Gwamnonin APC na wata ganawa da shugaban jam’iyyar, Sanata Abdullahi Adamu gabanin zaben gwamnoni da na ’yan majalisar dokoki da ke tafe a ranar Asabar.

Dukkan mambobin Kwamitin Zartaswa na jam’iyyar na halartar taron na sirri da ke gudana a shelkwatar jam’iyyar da ke Abuja.

Yawancin gwamnonin jam’iyyar ta APC na neman yin tazarce a zaben da ke tafe a ranar Asabar, yayin da kuma wasunsu sun sha kaye ko kuma sun samu nasarar zama zababbun Sanatoci a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu.

Sakataren jam’iyyar APC na Kasa, Iyiola Omisore; Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa kuma dan takarar gwamnan Jihar Delta a jam’iyyar, Sanata Ovie Omo-Agege; Dan takarar gwamnan APC a Jihar Ribas, Tonye Cole; Abubakar Sadiq, tsohon hafsan hafsoshin sojin sama, wanda shi ne dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a Bauchi, na daga cikin wadanda suka halarci taron.

Haka kuma, gwamnonin jihohin Kebbi Atiku Bagudu da na Jigawa Abubakar Badaru da kuma na Zamfara na cikin wadanda ke halartar zaman.