A cikin addu`ar ban kwana ta barin mulki da aka shirya wa Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan da uwargidansa Dame Patience Jonathan a wata Majami`a da ke unguwar Kubwa ta kewayen babban birnin tarayya Abuja a waccan lahadin da ta gabata, an ruwaito Shugaban a cikin jawabinsa yana gargadin Ministocinsa da sauran mataimakansa a kan lalle su zama cikin shirin fuskantar kuntatawa da takurawa daga sabuwar gwamnatin APC da za ta gaji gwamnatinsa a rana irin ta yau in Allah ya kai mu. A wajen ya yi ta nanata irin halin da za su shiga shi da makarraban nasa, wanda ya ce duk ba wani abu zai jawo masu haka ba, sai don irin sadaukarwar da suka yi cikin bautawa kasar nan cikin shekaru biyar da suka dana mulkinta.
Shugaban ya fadi cewa “A lokacin da mutum yake kan karagar mulki, zai iya daukar matakin da zai kyautata wa mafi yawan al`umma, amma kuma zai iya shafar wasu ta fannoni daban-daban wadanda ka dauki hushi da kai. Don haka Ministocina da mataimakana da muka yi aiki tare, da ni kai na, ina tausaya mana, don kuwa za mu fuskanci kuntatawa da musgunawa. Don haka mu zama cikin shirin fuskantar wannan kalubale. Ga Ministocina ina maku fatan da na ke yi wa kaina, Ministoci za su fuskanci mawuyacin hali. Dukkanmu za mu fuskanci mawuyacin hali. Makomarmu za ta zama mai wahala”. Inji Shugaba Jonathan, a lokacin waccan taron addu`a.
Ya ci gaba da cewa “ Shi mutum ne da yake cikin farin cikin cimma burinsa a rayuwa, inda ya kara da cewa tafiyar da mulkin kamar yadda ya yi a kan daidaita al`amurran kasar nan da irin nasarorin da ya samu matakai ne masu tsada, wadanda yake shirye da ya biya.” Ta bakin Shugaban kasa Jonathan ke nan. Wani batu da ya sake nanatawa a wajen waccan addu`a shi ne irin wai yadda ya karvi kaddarar ya fadi zaven ranar 28 ga watan Maris din da ya gabata, ba tare da ya yi shawara da kowa ba, abin da ya ce ya yi don tabbatar da dorewar mulkin dimokradiyyar kasar nan da zaman lafiyarta. Matsayin da ya ce mutane da yawa, musamman na kusa da shi da bai ambata sunanyensu ba, sun ta ganin baubaucinsa.
A dai wata addu`ar bankwanar da aka shirya masa a Mujami`ar fadar Aso Villa, a Abuja, a ranar Lahadin wannan makon, Shugaba Jonathan ya yi amfani da wannan damar wajen neman afuwar `yan kasa da ya savawa a cikin tafiyar da gwamnatinsa. Yana mai jaddada cewa “A lokacin da kake kan mulki za ka dauki wasu matakai bisa ga abin da ya bijiro maka, kuma ba lalle ne su yi wa wasu dadi ba, ga irin wadannan mutane ina neman afuwarsu, ba da gangan koda ganganci na yi haka ba, sai don yanayin da ya bayyana a lokacin.” Inji Shugaba Jonathan.
Masu iya magana kan ce akwai ranar kin dillaci, wai ranar da rigar Sarki ta vata. Daga irin wadancan kalamai na Shugaba Jonathan na shi da Ministocinsa da sauran mukarrabansa za su shiga tasku bayan sun bar mulki, da kuma irin yadda Shugaban yake ta nanata ya amince da sakamakon ya sha kayi har ya buga wayar taya murna ga sabon zavavven Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari, tamkar a kidime ko a gigice ya yi su. Kuma suna kara nuni da cewa bai shirya barin mulkin ba a wannan lokaci. Idan ba haka ba, ya ya Shugaba Jonatahan zai kasa sanin irin koma bayan da gwamnatinsa ta samu a kan tavarvarewar fannoni irin na tsaro, da batun rikicin `yan kungiyar Boko Haram, kar ka yi batun garkuwa da sace mutane da ya game kasa.
Ta fannin tavarvarewar tattalin arzikin kasa nan ma babu kama hannun yaro a cikin gwamnatin ta Shugaba Jonathan ta shekaru biyar, kama daga fasa bututun man fetur da satar danyen man fetur da ta kai ganga 400,000, a kullum da uwa uba cin hanci da rashawa da ya yi kamari a cikin Ma`aikatu da Hukumomin gwamnatin tarayya, da rashin aiyukan yi musamman tsakankanin matasa. Ka iya cewa Shugaba Jonathan ya gaji wasu daga cikin wadannan matsaloli, amma barinsu su tavarvare shi ne babbar gazawarsa. dauki kuma batun irin yadda ya rika fifita `yan kabilarsa ta Ijaw da yankinsa na Neja Dela a dukkan wasu batutuwa na kasa. `Yan kasa kuma sun gani sun kuma ji irin yadda tsohon Neja Delta kuma jagoran `yan kabilar Ijaws Cif Edwin Clark da Alhaji Asari Dokubo da sauran tsagerun Neja Delta,suka yi ta cin karensu ba babbaka wajen kare Shugaba Jonathan da gwamnatinsa da la`antar `yan Arewacin kasar da suka rika yi wa gwamnatin Jonathan hannunka mai sanda ko nunin gyara kayanka, amma da rana daya shugaba Jonathan bai tava tsawatawa mutanen nasa ba, bare ya ce sun yi ba dai-dai ba. dauki irin yadda Shugaba Jonathan karara a kan son bukatarsa ya rika rura wutar bambancin addini da na kabilanci da na jinsi, koda daga zavo Wakilan taron da ya yi a shekarar bara, taron da dama wasu suka ce varnar kudi ne.
Haka labarin yake cikin tafiyar da gwamnatin Shugaba Jonathan, ka dauki batun tsohuwar Minisatar kula da Harkokin zirga-zirgar jiragen sama Uwargida Stella Odua da yanzu ta ci zaven zama `yar Majalisar Dattawa, wadda aka zarga da sayo motocin sulke guda uku a kan farashin da ya nunka har sau uku,kudaden da ba sa cikin kasafin kudin kasa na wannan shekarar. Maimakon a ce tun a wancan lokacin Hukumar hukunta masu ta`annati da kudaden jama`a ta EFCC ta gurfanar da Madam Odua gaban kuliya, sai kawai ta sauka salin-alin, yau kuma maganar da ake tana zaman jiran a rantsad da ita a zaman sabuwar `yar Malisar Dattawa.
Mai karatu akwai tavargaza da katovara iri-iri ta mulki da Shugaba Jonathan da mukarraban gwamnatinsa da na kusa da shi suka aikata a zamanin mulkinsa. dauki batun vacewar kudaden man fetur Dalar Amurka N200biliyan da tsohon gwamnan Babban Banki mai martaba Sarkin Kano na yanzu Alhaji Muhammadu Sanusi na II, ya yi kururuwar sun vace a wancan lokacin, amma maimakon Shugaba Jonathan ya duba sai kawai ya sallame shi daga kan mikaminsa. Ya Ilahi, yaushe za ka ce dukkan wadannan miyagun ayyuka da suka shafi al`ummar kasa ka ce kawai a kau da kai a kansu. Ai dama a zaune take ga duk wani mai mulki ya san cewa akwai ranar da wata gwamnatin za ta yi wa gwamnatinsa hisabi. Don haka ya zama wajibi Shugaba mai jiran gado Janar Muhammadu da ya ce gwamnatinsa za ta ja layi a kan binciken gwamnatin da zai gada ya canja ra`ayinsa a kan haka. Riga malam masallaci da Shugaba Jonathan ya yi don neman tausayawar `yan kasa, ko kadan bai kamata ta sa gwamnati mai shigowa ta kau da kai ba. Lalle ta bincika. Wurin da ba rami me ya kawo rami?