✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaba Buhari zai yi kwana 10 a Ingila

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya tafi Birtaniya domin gudanar ziyara ta kashin kansa bayan ya kaddamar da ayyukan raya kasa a Jihar Borno da ke…

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya tafi Birtaniya domin gudanar ziyara ta kashin kansa bayan ya kaddamar da ayyukan raya kasa a Jihar Borno da ke Arewa maso Gabas a jiya Alhamis.

Wata sanarwa da mai ba Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Watsa Labarai, Mista Femi Adesina ya fitara jiya Alhamis, ta bayyana cewa Shugaban ya kaddamar da ayyukan ci gaba a fannonin ilimi da lafiya da hanyoyi, a Jihar Borno inda daga nan ne ya kama hanyarsa ta zuwa Birtaniya a jiya Alhamis.

Tafiyar ta Shugaban Kasa tana zuwa ne kwana daya bayan da ya kaddamar da wasu ayyukan raya kasa a Jihar Legas.

Sanarwar ta bayyana cewa Shugaba Buhari zai dawo Najeriya ce a ranar Lahadi 5 ga watan Mayun bana, wato zai shafe tsawon kwana 10 a Birtaniya ke nan.

Sai dai sanarwar ba ta bayyana takaimaiman abin da zai kai Shugaba Buhari Birtaniyar ba, amma wata majiya ta ce watakila zai huta ne don ya samu sukunin fuskantar zango na biyu na mulkinsa.

A kwanakin baya Shugaba Buhari ya kai ziyara kasashen Gabas ta Tsakiya wato Jordan da Katar inda ya gabatar ta makala mai taken “Shimfida hanyar zuba jari domin habaka tattalin arzikin duniya a zamanance.”

Kuma, kwana biyu kafin tafiyarsa zuwa kasashen Gabas ta Tsakiya, Shugaba Buhari ya je kasar Senegal, inda ya halarci bikin rantsar da Shugaban Kasar Macky Sall a karo na biyu.

A shekarar 2017 Shugaba Buhari ya kwashe fiye da wata uku a yana jinya a birnin Landan na kasar Birtaniya, inda a wancan lokaci Mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranci kasar a matsayin Mukaddashin Shugaban Kasa.

’Yan adawa da wadansu ’yan Najeriya suna yawan sukar yawan tafiye-tafiyen da Shugaba Buhari yake yi zuwa kasashen waje, inda suke cewa bai kamata ya rika fita ba musamman ganin yadda ake fama da matsalar tsaro a sassan kasar nan.