✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaba Buhari ya nada sabon Sufeto Janar na ’yan sanda

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nada Adamu Mohammed a matsayin sabon Sufeto Janar na ‘yan sanda Najeriya. Bashir Ahmed ya wallafa a shafinsa na tiwita…

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nada Adamu Mohammed a matsayin sabon Sufeto Janar na ‘yan sanda Najeriya.

Bashir Ahmed ya wallafa a shafinsa na tiwita inda ya sanya hoto mai dauke da Ibrahim Idris da Adamu Mohammed, sannan ya rubuta cewa, “tsoho da sabon Sufeto Janar na ‘yan sanda.”

Shi dai Ibrahim Idris ya sauka bayan ya kai shekara 60 a duniya, inda dokar kasa ta tanadar da dacewar yin ritaya.