Tun bayan da wani lauya ya janye karar da ya shigar a kotu, wadda ita ce sanadin haramta mukabala a tsakanin Shaikh Abduljabbar Nasiru Kabara da wasu daga cikin malaman Kano, wata tambaya da ke ta kai-kawo a zukatan mutane da danma ita ce yaushe za a fuskanci juna?
Bayan nan kuma sai tambaya ta biyu ta biyo baya: anya malaman za su iya ja da malamin, wanda ake ta caccaka bisa zargin yin batanci ga Ma’aikin Allah?
- ’Yan Bindiga Sun Kashe Mai Gari A Sakkwato
- An Janye Karar Da Ta Hana A Yi Mukabalar Sheikh Abduljabbar
Yanzu dai Gwamnatin Jihar Kano ake jira ta sanar da ranar da za a yi ta ta kare tsakanin malaman na Kano da Shaikh Abduljabbar, wanda suke zargi da gurbata akidar mutane da kuma yin batanci ga Sahabbai da wasu Magabata na Kwarai.
Shaikh Abduljabbar dai ya kekasa kasa cewa shi a kan gaskiya yake, hasali ma, kare Fiyayyun Bayin yake yi.
A baya ya kalubalanci duk malamin da ke ja ya fito a baje-kolin hujjoji, gaskiya ta yi halinta, kuma malaman suka ce masa Bismillah.
Saboda haka ne Gwamnatin Jihar Kano dai ta shirya mukabala a tsakaninsa da malaman, kuma bangarorin sun amsa goron gayyatar, amma kotu ta hana.
Gabanin haka, gwamnatin ta dakatar da shi daga yin kowacce irin da’awa sannan ta rufe majalisi da masallacinsa.
Kure Abduljabbar
Wasu na ganin malaman na da jan aiki a gabansu na samu su titsiye shi har su iya kure shi.
A cewar Abdulrahman Jibril, wani mazaunin birnin Kano, Abduljabbar ba kanwar lasa ba ne, “duba da irin shirin da nake tunanin ya yi da kuma irin kwarin gwiwar da yake nunawa.”
Shi ma wani mazaunin birnin na Kano da ya nemi a boye sunansa ya ce, “Ana gab da mukabalar da kotu ta dakatar da farko, sai da Abduljabbar ya jibge litattafai a cikin mota a-kori-kura da zai kafa hujja da su a zaman.
“Uwa-uba, za a kara da shi ne fa a kan abin da ya sani, yake koyarwa, yake kuma da’awa a kai, har litattafai ya rubuta, don haka ba da ka zai yi magana ba.”
Wani bawan kuma mai suna Muhammad Saleh cewa ya yi ba ya tare da akidar Abduljabbar, amma “kar ka manta tun farko shi ya ke ta neman a zo a yi mukabala da shi.
“Akwai abin da ya taka sannan ina kyautata zaton akwai abin da yake neman cimmawa.”
Ya kara da cewa, “Sannan kuma ba wanda ya san shi irin tambayoyin da ya shirya yi wa malaman, balantana su shirya irin amsoshin da za su ba shi.”
Zilliyar Abduljabbar
“Wani kalubale kuma”, inji Sani Sha’aya’u, shi ne yadda malaman za su iya titsiye shi da murya daya, ka san yadda a baya ta kasance tsakaninsa da wasunsu da suka yi mahawara da shi a kan mas’alar.”
Akwai hotunan bidiyo da ke nuna yadda Shaikh Abdujabbar ya fafata da wasu malamai.
A daya daga cikin hotunan bidiyon, an ga yadda ta kaya a muhawararsa da wani malami wanda ya ba litattafan da ya wallafa kan maudu’in, ya je ya yi nazarin su, ya fito da kurakuran da yake ganin Shaikh Abduljabbar ya yi, sannan su yi mukabala.
A zamansu, malamin ya zo da mas’aloli da dama, ya nemi a warware zare da abawa, amma Shaikh Abdujabbar ya ce tun da malamin ya gano mas’alolin, to ya bijiro da su, shi kuma zai je ya yi nazari a kansu, sannan a sake sa lokaci ya mayar da martani.
Hakan ta sa ake ganin da wuya a iya cimma wani abu a zaman da za a yi.
‘Za a wujijjiga Abduljabbar’
Sai dai wasu na ganin Shaikh Abduljabbar zai kwashi kashinsa a hannun malaman da suka dade suna neman yin karon batta da shi.
Rabiu Ibrahim ya shaida wa Aminiya cewa, “Shi kanshi ya san ba a kan daidai yake ba, amma na san malaman sun ishe shi, duk da taurin kansa.
“Kar ka manta malaman nan duniya ta san su, kuma ko an ki, ko an so, gwanaye ne, ba kuma a shakkar tsantseninsu da zurfin iliminsu”.
“Wasunsu fa malaman addini ne a jami’a kuma a kasashen waje suke yi; ni a gani na, mutum daya ma a cikinsu ya yi wa Abduljabbar yawa,” inji Khalid Yakubu, wani mzaunin unguwar Kabuga a Kano.
‘Bata lokaci ne’
Tuni dai wasu malamai suka bayyana cewa tsayawa yin mukabala da Abduljabbar bata lokaci ne, kuma ba shi da amfani.
Idan ba a manta ba, kungiyar Jama’atu Nasril Islam ta nesanta kanta da mukabalar wadda ta ce ba ta da masaniya a kan yadda aka shirya ta da kuma tsarin da za a bi wurin gudanarwa.
Babban Sakatarenta, Dokta Khalid Aliyu Abubakar, ya ce tun asali bai ma kamata Gwamantin Kano ta bai wa wanda ake zargin irin kulawar da ya samu ba, har yake ganin kansa tamkar wani gwarzo.
Ita ma kungiyar Izala (JIBWIS) ta ce ba za ta halarci zaman da za a yi ba, kuma ko wakilanta a kananan matakai ma ba za su halarta ba.
Tsarin mukabalar
Kawo yanzu dai ba a kai ga sanya ranar mukabalar ko tsarin gudanar da ita ba.
Amma a tsarin da Gwamnatin Kano ta yi na farko, an bai wa wadanda za su yi mukabalar mako biyu su tattara bayanai da maudu’an da za su tattauna a kai.
Kungiyoyin addini kuma za su turo wakilansu wurin mukabalar, sannan za a gayyato wasu manyan malamai daga wajen Jihar Kano su shaida yadda za ta kaya.
A yanzu dai ba a sani ba ko Gwamnatin za ta sake saka lokaci, ko kuma za ta riki hujjar masu adawa da mukabalar ta shashantar da zancen.