✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Shin ko kun san wanda ya sayi Bankin Polaris?

Mamallakin bankin ya biya naira biliyan 50 kudi hannu.

Bayan cece-kuce da gutsiri tsoma, Babban Bankin Najeriya CBN ya sanar da sayar da bankin Polaris ga kamfamin SCIL kan tiriliyan 1.35.

CBN ya sanar da sayar bakin ne a karshen makon jiya, bayan da kamfanin ya biya naira biliyan 50 kudi hannu, sannan zai biya cikon a wa’adin da aka ba shi.

Lawan Auwal Abdullahi shi ne mai kamfanin SCIL da ya yi wannan cinikin da ya dauki hankalin jama’a da ya kashe bakin tsanya.

Dangartakar sa da Babangida

Alhaji Lawan surukin Ibrahim Babangida ne, shi ne wanda ya auri Halima, ‘yar tsohon Shugaban Kasar ta biyu a  watan Mayun shekarar 2017.

Ga wadanda za su iya tunawa, shi ne wanda bikin daurin auren ya ja hankalin ‘yan jaridu na ciki da wajen Najeriya saboda kasaita.

Domin kananan jiragen akalla 30 na mahalarta bikin ne suka sauka a filin jirgin saman Minna, babban birnin Jihar Neja.

An kuma gudanar da bukukuwa daban-daban har guda 9, na kuma tsawon kwanaki 4 a jihohin Neja da Gombe, a inda rahoton jaridu ke cewa an kashe a kalla Naira miliyan 30.

A lokacin auren, attajirin ya bayar da Naira 500,000 da kuma shanu 10 a matsayin sadaki,

Sannan yana da wasu matan uku a lokacin.

Kasuwancin sa

Baya ga kamfanin SCIL na kasuwanci da zuba jari, attajirin na da wasu kamfanoni manya guda biyu, in ji jaridar kasuwanci ta Prime business Africa.

Duk da cewa ya dade a harkar kasuwanci, babu wanda ya san cewa attajirin ya kwashe sama da shekara 10 ya na harkar mai da gine-gine da ayyukan gona da kuma kasuwancin kasa da kasa.

Kamfanin SCIL a watan Afrilun wannan shekara aka yi masa rajista. Gwamanti ta kuma sayar masa bakin Polaris ne ta hannun Hukumar Kula da Kadarorin Gwamnati da Kwato Bashi AMCON.