✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Shin da gaske cin wake ga mace mai juna biyu yana sa jariri ya yi kato sosai?

Ga abin da masana kiwon lafiya suke cewa a kan batun

A shirin Aminiya na Lafiyar Mata da Yara, a wannan makon, likitanmu, Dokta Auwal Bala, ya amsa wata tambaya ce da ta fito daga daya daga cikin masu bibiyarmu mai suna Zainab Muhammad.

Ta yi tambayar ce a kan gaskiyar cewa mace mai juna biyu idan tana yawan cin wake dan cikinta zai zama kato sosai. Ga amsar likita:

Amsa: Eh, ana samun tambayoyi da dama ire-iren wadannan.

Abin da mata masu juna biyu suka fi tambaya akai shi ne wai ko milo yana sa jaririn da ke ciki ya yi kato a kasa haifo shi?

A hakikanin gaskiya duk da cewa jarirai na bukatar abinci a ciki, ba abinci ne ke kan gaba wajen sa yara su zama katunkatun a ciki ba, gado ne. Idan uwa ko uban manya ne, to ana kyautata zaton jaririn ma kato ne.

Duk wani abinci da mace za ta ci idan ba gadon girma jaririnta ya yi ba, ba zai zama kato ba sai dai madaidaici.

Akwai kuma ciwo daya da kan sa jarirai da ke ciki kuma su zama manya-manya. Wannan ciwo shi ne ciwon suga. Amma ban da wadannan ba abin da zai sa jaririnki ya yi girman wuce hankali.