✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shin da gaske ana iya warkewa daga ciwon makoko ba sai an yi tiyata ba?

Shin da gaske ne ana iya warkewa daga ciwon makoko da magunguna kadai ba sai an yi tiyata ba? Amsa: Eh, kwarai haka ne. Akwai…

Shin da gaske ne ana iya warkewa daga ciwon makoko da magunguna kadai ba sai an yi tiyata ba?

Amsa: Eh, kwarai haka ne. Akwai cututtukan makoko da kwayoyin magani ne kawai zai sa  ya daina girma ko ya shanye, akwai wadanda kuma sai an yi musu tiyata an dan yade wani bangare na makokon saboda kwayoyin maganin ba su sa makokon ya daina girma ba, ko makokon yana girma yana danne makoshi. To idan aka ga haka shi ne ake tura mai matsalar bangaren tiyata. Kai a wadansu ma ruwa ciwon yake durawa, a wadansu kuma rikidewa yake ya zama daji, wadanda wadannan dole sai an yi tiyata ake magance su.

Dama ai ka san abin da ke kawo makokon ko? Akwai wata ’yar halitta a wuya karkashin fata karama. Wannan halitta tana samar da wani sinadari da ake kira thyrodine wanda ke taimaka mana wajen abubuwa da dama kamar jin dumi da sarrafa abinci da sauran abubuwa da dama. Wannan sinadari ba a iya sarrafa shi sai da wani sinadarin kuma na aidin wato iodine wanda ake samu a ruwan sha da kifi da yagot da wake. A da a wasu kauyukan da ruwan shansu babu wannan sinadari za a ga mutane da yawa masu makoko. Amma yanzu da yake ana kara wannan sinadari cikin gishirin da muke ci yau da kullum, za a ga matsalar ta ragu. Da can an fi samu a mutanen da ke kasar Filato da Taraba sun fi samun wannan matsala saboda ruwan shansu na tsaunuka ne wanda ke da karancin aidin. Amma yanzu abin ya yi sauki. 

To a mafi yawan lokuta, idan ba wannan aidin a abincin mutum sai makokon wuya ya fara girma. Da an yi amfani da ruwa mai aidin ko kifi ko gishirin da aka kara wa aidin din sai wurin ya sabe.

Idan ina cin abinci ko mai sanyi ne kuwa sai na yi zufa, kuma ko lokacin sanyi ne. shi ne nake tambaya ko wannan ciwo ne?

Daga A.A Chibiyayi

Amsa: Eh, kwarai wannan bai kama da lafiya ba, ya fi kama da rashin lafiya. Akwai wani ciwo a likitance da ake kira Frey Syndrome da ya yi kama da wannan matsala taka. Amma a wannan ciwon na likitanci, sai idan an taba wa mutum tiyata ko ya taba jin ciwo a fuska shi ne zai iya samun wannan tangarda ta zufa a fuska kawai yayin cin abinci. Idan kana son karin bayani da bincike ko wannan matsalar ce da kai to ka tuntubi likita ku zauna ido-da-ido.

Me ke sa mutum yawan zufa wasu lokuta ma a tafin hannu ko a tafin kafa?

Daga Usman danbaba da Dirai Damuwa

Amsa: Ita ma wannan a likitance matsala ce da akan kira hyperhidrosis, wato yawan zufa. Masu matsalar suna samun yawan zufa a ko’ina a jikinsu har ma inda mutane ba su cika zufa ba kamar tafin hannuwa da na kafa. Ita ma wannan matsala mai ita yana da bukatar ganin likitan fata.

Ni kuma a lokuta daban-daban nakan yawan jin cibiyata tana tsikarata. Ko me ke kawo hakan?

Daga Sani Umar, Malumfashi

Amsa: Eh, a likitance akwai cututtukan ciki da akan fara jin alamunsu ta wajen cibiya kafin daga bisani su bar wurin su koma wurinsu na asali. Suna da dan dama irin su apendis da kaba da sauransu, amma mukan bambance su ne idan marar lafiya ya fadi sauran alamun da yake ji, ba kawai ciwon ba. Misali sai likita ya tambaya ko akwai kumburi ko gudawa ko amai ko tashin zuciya ko rashin iya cin abinci, ya kuma duba cikin gaba daya sa’annan zai iya tabbatarwa ko akwai matsala ko babu. Don haka ke nan kana bukatar likita ya duba ka.

Na kasance cikina kullum a kumbure ko na ci abinci ko ban ci ba. Me ke kawo haka?

Daga Fatima danzomo

Amsa: Ya danganta, kumburin da amai ko da gudawa, yana sacewa ko ba ya taba sacewa. Domin akwai matsaloli da dama da kan iya kawo irin wadannan alamu amma za mu iya bambancewa idan kika je asibiti aka yi tambayoyi aka tantance wane ne a cikinsu. Ke nan ba lafiya ba ce kumburin ciki kullum, abin na bukatar ganin likita.

Ni kuma idan na ci yaji sai in fara shakuwa. Ko meke kawo hakan?

Daga Babangida ’Yargaya

Amsa: Idan ni ne kai yadda zan yi idan ina so na san ko yaji ne ke kawo min yawan shakuwar ko wani abu daban, sai in daina cin yaji na tsawon wata in gani ko zan ci gaba da irin shakuwar. Idan na tsayar da cin yaji ban ci gaba da shakuwa ba, to na san tabbas yaji ne ke kawo min ita, kuma alamar cewa cikina ba ya son yajin. Idan kuma na tsaida yajin amma yawan shakuwar ba ta ragu ba, to na san ba yaji ba ne ke kawo min shakuwar wani abu ne daban, don haka sai in tuntubi likita.

Ko ’ya’yan giginya suna da amfani ga lafiya?

Daga Ali A.D

Amsa: Eh, don ma kusan giginyar wannan kasar tamu ta Arewa ta dauki hanyar karewa ba a bincike a kanta sosai. Amma dai a kasashen da har yanzu suke da ita da yawa irin su Indiya da Sri Lanka binciken da suka yi a kan ’ya’yan ya nuna giginya ’ya’yanta kamar sauran ’ya’yan itatuwa suna da amfani domin akwai sukari da sinadarai na fibre da na ma’adinan iron da magnesium da calcium a ciki.

Na taba karanta wani rubutunka a kan ciwon fargaba. To ni tawa fargabar sai na zo magana a cikin mutane. Shi ne nake neman shawarwari.

Daga Abubakar Adam

Amsa: Wannan ita ce karama a cikin matsalolin fargaba, domin fiye da rabin mutane ba sa iya magana cikin mutane ba da tsoro ko fargaba ba. Amma hanyar da ake bi a shawo kanta ita ce ta bita. Wato ka sa kanka gaban abokai ko ’yan uwa ko ’ya’ya wadanda ba za ka ji shayinsu ba, ka yi ta bitar magana doguwa a gabansu. Idan kana haka na tsawon watanni abin zai ragu.