Kusoshin jam’iyyar PDP da suka fice daga APC mai mulki gabanin zaben 2019 sun yi fatali da kiran da APC ta yi musu cewa su dawo cikinta.
Komawar tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara, da Sanata Barnabas Gemade APC ya ba da hasken zawarcin kusoshin kafuwar jam’yyar da suka fice, sai dai mataimakansu sun ce hakan ba mai yiwuwa ba ne.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da tsohon Shugaban Majalissar Dattawa, Bukola Saraki da kuma tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso na daga cikin wadanda APC ke son dawowa.
A wata sanarwa da jam’iyyar APC ta fitar a ranar Lahadi, ta ce shirye take ta karbi sabbin ‘yan jam’iyya da wadanda suka fice da ke son dawowa cikinta.
— Ya za a yi Atiku ya koma APC?
Amma kakakin Atiku, Paul Ibe, ya shaida wa wakilinmu ta waya ewar “Ba gakiya ba ne, babu wanda ya tuntubi Mai gida, Mai Girma Atiku ba zai koma cikin” jirgin da zai nutse ba”.
“Duk wadannan abubuwan suna yi ne don kawar da hankalin ‘yan kasa daga gurbataccen mulkin gwamnatinsu da ta jefa mutane cikin kangin talauci da ya mayar da Najeriya cibiyar talauci.
“Mulkinsu na shekara biyar ya kara jefa kasar nan cikin rashin tsaro da rarrabuwa kawuna fiye da kowane lokaci. Sa’annan tsarin mulkinsu ya jefa mutane cikin rashin aikin da rashin kishin kasa.
—Komawa APC tamkar yunkurin shiga bala’i ne
A nashi bayanin, Saraki, ta bakin wani mataimakinsa da ya nemi a sakaya sunansa ya ce kiran na APC dabara ce ta kawar da tunanin daga rikice-rikicen jam’iyyar da kuma gazawar gwamnatin Buhari.
“A lura cewar matsalar Dogara da Gwamnan Bauchi ce ta sa ya koma APC, kuma babu wata matsala tsakanin maigidana da Dogara kan komawarsa APC. Sai dai PDP ta fi APC nesa ba kusa ba. Babu mai sha’awar APC a yanzu”, inji shi.
—APC ta kama hanyar rugujewa
Mai Magana da Yawun Kwankwaso, Kwamaret Aminu Abdussalam, ya ce babu dan siyasa mai hankali da zai yi kuskuren komawa APC.
“APC gab take da tarwatsewa kuma a iya sanina, babu wani da ya tuntubi Maigirma Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso wanda cikakken dan PDP ne.
“Kuma ya za a yi mutumin da ke cikin hankalinsa ya shiga jam’iyyar APC?.
“APC ta hau hanyar rugujewa, ‘ya’yanta sun raunata ta kuma babu wata hanya da za su bi su gyara ta.
“Sun lalata komai tare da dagule harkar tsaron kasar nan. A shekara biyar da suka kwashe suna mulkinsu babu abun da suka yi sai azabtar da mutane”, inji Abdussalam.
Dawowar Dogara alheri ne —APC
A wannan gabar, masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC na kananan hukumomin Bogoro da Tafawa Balewa da Dass a jibar Bauchi sun bayyana dawowar Dogora jam’iyyar a matsayin alheri.
A taron yan jarida da jam’iyyar da yi a Bauchi, shugaban masu ruwa da tsakin jam’iyyar, kuma tsohon shugaban karamar hukumar Bogoro, Elisha Gwamis, ya ce komowar Dogara jam’iyyar APC za ta ba su damar lashe zaben kananan hukumomin da za a yi a watan Oktoba.