Ko shakka babu idan mutum yana son haduwa da Allah Madaukaki lami lafiya, zai rika yin ayyuka nagari domin haduwa da Shi lafiya, zai yi tattalin wannan haduwa ta aikata ayyuka nagari, ayyukan kirki, ayyukan da ko ’yan uwansa mutane za su ce ala sambarka. Wanda kuma ba ya son haduwa da Allah lami lafiya zai tafiyar da rayuwarsa ce cikin sabon Allah. Ba zai so haduwa da Allah (Subhanahu Wa Ta’ala) ba, kuma Allah ba zai so haduwa da wannan bawa lami lafiya ba.
Na shida: Mu kawar da duk wani abu da zai shiga tsakaninmu da Allah Madaukaki. Kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya umarce mu cewa mu yi dubi da idon basira kan kowane al’amari da muke yi, mu guji duk abin da ya saba wa Allah. Kuma duk wanda kake son haduwa da shi lami lafiya wajibi ne ka kauce wa duk abin da ba ya so.
Na bakwai: Kullum mu sanya Annabi (SAW) a gaba wajen koyi da shi, domin Allah Ya sanya kaidi na sonSa kan yin biyayya ga Annabi Muhammad (SAW). Don haka sai mu bi koyarwarsa a ayyukanmu mu da mu’amalolinmu da duk wani motsi namu, mun sanya bukatunsa a kan bukatunmu, kafin mu kasance masoyan Allah, kuma Allah Ya so mu. Allah Madaukaki Ya ce: “Ka ce: “Idan kun kasance kuna son Allah, to, ku bi ni, sai Allah Ya so ku, kuma Ya gafarta muku zunubanku.” (k:3:31).
Na takwas: Wajibi ne mu rika yin hakuri a cikin al’amuranmu. Mu yi hakuri wajen yin biyayya ga umarnin Allah da ManzonSa (SAW), kuma mu yi hakuri wajen danne zukatanmu daga saba wa Allah. Kuma mu rika hakuri a duk harkokinmu, kamar a mu’amalarmu da iyalai da mu’amalarmu da makwabta da mu’amalarmu da abokan zama ko abokan aiki kai koda haduwa ka yi da mutum a kan hanya, ka yi hakuri kan saba maka da zai yi. Mu yi hakuri kada mu cuci kowa, idan kuma waasu suka cutar da mu mu yi hakuri kada mu rama, idan ba za mu iya hakuri ba, to wajen ramuwar kada mu wuce iyaka. Malamai sun ce idan mutum ya rika yin hakuri a mu’amalarsa da mutanen gidansa da makwabtansa da abokan aikinsa, sai ya zama As-sabiru (mai yawan hakuri). Kuma Allah Madaukaki Ya gaya mana game da masu hakuri cewa: “Kuma Allah Yana son masu hakuri.” (k:3:146). Ke nan hakuri na jawo Allah Ya so mutum, idan haka ne rashin hakuri yana jawo Allah Ya ki mutum ke nan.
Na tara: Wajibi ne mu sani cewa Allah Madaukaki Yana da sunaye da siffofi masu kyau (Asma’ul husna was-siffatihi). Don haka a duk lokacin da muke karanta Alkur’ani Mai girma muka ci karo da kalmar Ar-Rahman wajibi, ne mu fahimci hakikanin ma’ana da manufarta kuma mu sa ran Allah Madaukaki Ya yi mana rahama. Sannan idan muka ci karo da kalmar Assami’u ko Albasiru wato Mai ji ko Mai gani, wajibi ne mu fahimci cewa Allah Yana ji kuma Yana ganinmu a kowane lokaci, don haka mu rika taka-tsantsan a duk abin da za mu aikata ko za mu furta. Kuma idan muka hadu da kalmar Shadidul ikabi, Mai tsananin ukuba, to, mu sani Allah Ya fi kowa yin ukuba, don haka mu tsaya mu yi tunani kafin mu saba wa Allah, don mu kaurace wa wannan aiki. Idan muna kula da wadannan abubuwa za mu rage aikata wasu ayyukan barna da muke yi a yau da kullum.
Na goma: Mu ci gaba da yin nafilfili, wato ayyukan ibada da ba na farilla ba. Ya zo a cikin Hadisin kudusi cewa Manzon Allah (SAW) ya ce: “Allah Madaukaki Ya ce: “Bawa ba zai gushe ba yana kusantaTa ta yin nafilfili har sai Na so shi.”
A sharhin Hadisin malamai sun ce wadannan ayyuka na nafila sun kunshi kowane nau’i ne. Ya alla nafila ta harshe kamar zikiri da karatun Alkur’ani da hailala da fadin magana mai kyau da sauransu, ko kuma nafila ta gabbai kamar Sallah da Azumi da makamantansu, ko kuma ta dukiya kamar sadaka da kyauta.
Amma mutum kullum yana saba wa Allah, amma ya ce yana son Allah, akwai alamar tambaya a wannan so. Wani mawaki ya ce: “Ta yaya za ka saba wa Allah, sannan ka ce kana son Allah?”
Wannan ’yar nasiha wata hanya ce ta fahimtar wannan so da Allah Yake maka ko kai kake maSa. Domin idan soyayyarka ga Allah ta gaskiya ce, wajibi ne ka yi maSa biyayya. Kuma hakika duk wanda ke son wani ba zai yi abin da zai bata masa rai ba, sai dai wanda yake so ko kuma wanda zai dadada masa. To haka lamarin ya wajaba ya kasance a tsakanin bawa da Ubangiji. Kada bawa ya rika cewa yana son Allah amma ayyukansa su rika nuna sabanin haka. Idan bawa ya so Allah ya yi maSa biyayya sai soyayyar Allah ta tabbata a kansa, ya samu zaman lafiya da kwanciyar hankali da natsuwa a rayyuwarsa koda bai da miliyoyin Naira da Dala, amma idan bawa ya rika saba wa Allah sai ya rasa soyayyar nan ta Ubangiji, kuma sai a cire albarka da alheri a rayuwarsa ya kasa natsuwa ya rasa kwanciyar hankali koda yana matashin kai da Naira da Dala.
Allah a gare Ka muke kai kukanmu, Ka kwace mu daga mutanen nan azzalumai. Ka takaita jarrabawar da Kake yi mana a yanzu, Ka dawo mana da zaman lafiya a kasarmu da sauran kasashen Musulmi, Ya Allah ba domin halinmu ba, domin rahamarKa da tausaywarKa, ka dubi kananan yara da ake mayarwa marayu, Ka dubi raunanan mata da ake mayarwa gwagware, Ka dubi matasa da ake zubar da jininsu, Ka dubi dattawa da karfinsu ya kare suke bukatar tallafin ’ya’yansu da ake kashewa. Babu karfi babu dabara sai a gare ka.
Wasallallahu alan Nabiyil karim wa alihi.