Har yau kurwarsa na bin Arewa
A shekaranjiya Laraba ne aka cika shekara 20 da gwamnatin mulkin soja ta Janar Ibrahim Badamasi Babangida ta gudanar da zaben 12 ga watan Yuni, 1993, wanda dukkan al`umma da kungiyoyi na ciki da wajen kasar nan suka amince da sahihancinsa, har ma ana kyautata zaton shahararren Attajiri Cif M. K. O. Abiola na jam`iyyar SDP ne ya lashe shi, amma bisa ga wani dalili na Babangida sai ya soke shi.
Wancan zabe shi aka so ya kawo karshen mulkin soja na kusan shekara 10, amma maimakon haka sai ga shi ya mayar da hannun agogo baya da za a iya cewa har yanzu kurwar soke zaben na bin harkokin siyasar kasar nan, kuma Allah ne kadai ya san ranar da `yan Arewacin kasar nan za su fita daga kanginsa.
Ciki da wajen kasa, an yi ittifaki a kan sahihancin zaben 12 ga Yuni, 1993, ba don komai ba, sai don irin yadda `yan kasa suka ajiye bambance-bambancen addini da na jinsi da na kabilanci duk cewa ‘yan takarar daga bangare mabambanta suka fito, wato Cif Abiola na jam`iyyar SDP da Alhaji Bashir Othman Tofa na jam`iyyar NRC), suka taru wuri guda gwargwadon iko, suka kada wa Abiola kuri`un da aka yi ittifakin da an fadi sakamakonsa, to, kuwa da ba makawa shi zai lashe zaben.
Wani abin sha`awa kuma abin tarihi da zaben ya bari shi ne, irin yadda duk da kasancewar Cif Abiola da mataimakinsa cikin neman shugabancin kasar, wato Ambasada Babagana Kingibe, dukkansu Musulmi ne, shi kuwa Alhaji Bashir Tofa ya dauko Dokta Sylbester Ugoh a zaman mai rufa masa baya dan kabilar Ibo kuma Kirista, amma sai ga shi Kiristocin kasar nan sun ajiye batun addini gefe daya suka zabi tafiyar Cif Abiola da Ambasada Kingibe. Bayan wannan, hatta a Jihar Kano, inda Alhaji Bashir Tofa ya fito, rahotannin sakamakon zaben da aka soke sun tabbatar da cewa Cif Abiola ya ci Kano, wasu ma sun ce hatta sakamakon zaben mazabar da Alhaji Bashir Tofa ya fito ta Gandun Albasa, dan takarar SDP ya lashe.
Soke wancan zabe da gwamnatin Janar Babangida ta yi, shi ya yi sanadin `yan siyasa irinsu Cif Olu Falae dan takarar hadin gwiwar jam`iyyun AD da APP cikin takarar neman shugabancin kasa a zaben shekarar 1999, da Alhaji Ahmed Bola Tinubu tsohon gwamnan Jihar Legas yanzu kuma shugaban jam`iyyar ACN da irinsu Alhaji Sule Lamido Gwamnan Jihar Jigawa da Mista Labaran Maku Ministan Yada Labarai da mutane irinsu tsofaffin Hafsoshin soja Janar Alani Akinranade da Dan Sulaiman da dai sauran `yan gwagwarmaya don tabbatar da mulkin dimokuradiyya da taimakon kasashen waje suka yi ta matsa lamba don tabbatar da wancan zabe ga Cif Abiola, abin da ya kai har wasu suka kafa kungiyarsu ta NADECO, duk don ganin sai gwamnati ta tabbatar da zaben 12 ga watan Yuni. Wasu daga cikin wadannan mutane da na ambata da wadanda ban ambata ba saboda karancin fili, ta kai ga gwamnatin Janar Babangida da ta Janar Sani Abacha da ya hanbarar da gwamnati rikon kwarya ta Enest Shonekan a watan Nuwamban 1993, an daure su, wasu kuma zakara ya ba su sa`a suka yi gudun hijira zuwa kasashen waje.
Bayan gumu-ya-yi-gumu ne, Babangida a cikin watan Agusta, 1993, ya “koma gefe,” kamar yadda ya kira saukarsa, ya mika wa Cif Shonekan, wanda shi kuma bayan ’yan watanni a watan Nuwamba, 1993, Janar Abaca ya hambarar da shi ya kuma kori `yan Majalisun Dokoki na kasa da gwamnoni da `yan Majalisun Dokokin jihohi da Babangida ya sa aka zaba ya fara aiki da su a farkon shekarar 1992. Shi ma dai Janar Abaca haka ya yi ta fama da rigingimun `yan kungiyar NADECO da sauran `yan adawa masu gwagwarmayar ganin tabbatar da mulkin dimokuradiyya, har ya zuwa ranar 8 ga watan Yuni 1998, da aka wayi gari Allah Ya karbi kayansa.
Mutuwar Janar Abaca, ita ta kawo Janar Abubakar Abdussalami a kan karagar mulki, wanda ya sha alwashin mayar da mulki cikin watanni 11, don haka wadancan dai da suka soke zaben 12 ga watan Yuni suka kuma sake kullawa a zaman a faranta wa `yan kabilar Yarbawa rai, a bisa an sokewa dansu zabe, da kuma irin jajircewar da Yarbawan suka yi ta yi, tun da aka soke wancan zabe, musamman ta amfani da kafofin yada labaransu, cikin ruwan sanyi wadancan mutane suka sa gwamnati ta sako Janar Olusegun Obasonjo daga zaman sarkar daurin rai-da-rai, gwamnati ta yafe masa, kuma suka mika masa takarar neman shugabancin kasar nan kyauta a inuwar jam`iyyr PDP a zaben 1999, wanda ba wata wahala ya kasance daga gidan yari ya shige fadar shugaban kasa a bagas, wanda shi a lokacin mafarkinsa bai wuce a sake shi ba, ya koma gonarsa ta Otta.
Duk mai biye da yadda harkokin siyasar kasar nan suke suke gudana, akalla tun daga soke wancan zabe, zuwa wannan lokaci ya san cewa Arewa da mutanenta baya suka ci ba gaba ba, ta kowane fanni. Soke zaben ne ya yi sanadiyyar Obasanjo ya dawo karagar mulki har shekaru takwas ya mike kafa ya kuma yi yadda yake so, da tafiya tazame masa dole, ya dauko Alhaji Umaru Musa `Yar`aduwa (wanda aka san ba shi da koshin lafiya), ya damka masa mulkin, wanda bayan shekara biyu ta Allah ta kasance a kan sa, Arewa ta koma gidan jiya. Tun bayan zaben 2011, kowa yana ganin irin yadda Shugaba Jonathan da mutanensa na Neja Delta suke raina shugabannin Arewa, wadanda a da ko juyin mulki aka yi na soja su ake roka su rika.
A ra`ayina har yanzu kurwar zaben 12 ga watan Yuni 1993 na bin Arewa fiye da kowane yankin kasar nan, sai dai jajircewa ta gaskiya da addu`o`i kawai za su kai Arewa da mutanenta ga ci.