✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sheikh Ja’afar da Albani sun samu karramawa

Manyan malam da ’yan bindida suka kashe sun yi fice wajen gina rayuwar al'umma

Najeriya ta sanya fitattun malaman Musulunci a kasar, mariyagayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam da marigayi Sheikh Muhammad Auwal Albani, a cikin jerin mutum 60 da suka bayar da gudunmuwa wajen gina kasa.

Malaman biyu sun yi fice wajen yin wa’azin Musulunci da koyarwa kuma karatuttukansu sun ci gaba da karade sassan Najeriya da ma wasu kasashen har bayan rayuwarsu.

An tsara a fitar da jerin sunayen mutum 60 din da suka yi fice wajen gina kasa ne a cikin wani kundi na musamman da aka shirya a ci gaba da bukuwan cikar Najeriya shekara 60 da samun ’yancin kai.

Shugaban kwamitin kaddamar da kundin mai suna ‘Nation Builders at 60’, Dokta Abubakar Mohammed Sani, ya ce an tsara fitar da kundin ne domin yaba wa ’yan Najeriya da suka yi zarra a fannoni daban-daban wajen kawo cigaban kasa.

A jawabinsa ga ’yan jarida tare Shugaban Majalisar Editoci na aikin mai suna Project 6060.org, Akanimo Sampson, ya ce an yi aikin tsarawa da wallafa kundin mai suna ‘Project 60@60’ ne da hadin gwiwar madaba’ar Sprezzatura Publishing.

Babban Hafsan Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai; takwaransa na Rundunar Sojin Ruwa, Vice Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas; Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai; da tsohon Shugaban ’Yan Sandan Najeriya, Muhammad Dahiru Abubakar na daga cikin mutum 60 din.

Wasu ’yan Najeriyan da sunayensu suka samu shiga kundin sun hada da Shugaban Bankin Raya Afirka (AfDB), Akinwumi Adesina; Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Charles Soludo; da tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose.

Kudin zai kuma kunshi sunayen fitattun mata irinsu Fasto Bimbo Odukoya da Sanata Oluremi Tinubu.

Kazalika Dokta Ojo Onukaba, Zack Orji, tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani-Kayode, da Mai ba Shugaban Kasa Shawara kan harkokin Yada Labari, Mallam Garba Shehu, da sauransu.

A ranar Juma’a, 13 ga watan Afrilun 2007, wadansu ’yan bindiga da sanyin asuba, suka halarci masallacin da Shaikh Ja’afar Mahmud Adam yake limanci a Unguwar Dorayi, birnin Kano, suka iske shi yana jagorancin Sallar Asuba, suka harbe shi.

Shi ma Sheikh Muhammad Auwal Adam Albani Zariya wadansu ‘yan bindiga ne suka harbe shi tare da matarsa da dansa daya a ranar 1 ga Fabrairun 2014.