Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya caccaki lauyoyin da ke kare shi a shari’ar zargin shi da batanci ga Manzon Allah (SAW), cewa bai gamsu aikinsu ba.
A zaman kotun na ranar Alhamsi, Abduljabbar ya ce bai gamsu ba da yadda lauyoyin ke wa shaidun da aka gabatar a kamsa, saboda haka ya bukaci kotun ta ba shi dama ya yi wa shaidan tambayoyi.
Sai dai kuma alkalin Babban Kotun Shari’ar Musulunci da ke zaman ta a Kofar Fada a birnin Kano, Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola ya yi watsi da bukatar ta Abduljabbar.
Alkalin kotun ya kuma ba wa lauyan, Umar Mohammed, hakuri, ganin yadda kalaman malamin suka bata mishi rai.
– An fara gabatar da shaidu –
A ranar Alhamis aka fara gabatar da shaidu a shari’ar zargin Abduljabbar da yin batancin ga Manzon Allah (SAW) da kuma neman tayar da zaune tsaye a Jihar Kano, zargin da ya musa.
Tun da farko, lauyan Gwamnatin Jihar Kano da ta gurfanar da malamin, Farfesa Mamman Lawan Yusufari (SAN), ya gabatar da shaidansa na farko, Adamu Adamu, wanda ya ce shi dalibin Abduljabbar ne.
Adamu, wanda shi ne babban shaidan da aka gabatar ya shaida wa kotun cewa ya sha jin malaminsa Abduljabbar yana furta maganganun batanci ga Manzon Allah (SAW).
– Batancin da Abduljabbar ay yi –
A cewarsa, a ranar 10 ga watan Agusta, 2019 ya halarci karatun Abduljabbar a Masallacin Asshabulkhahfi da ke Gwale Filin Mushe inda Abduljabbar ke karatu, inda ya ji malamin yana furta kalaman batanci ga Manzon Allah (SAW) game da aurensa da matarsa Nana Safiyya (RA).
Ya ce ya sake jin malamin a ranar 20 ga watan Disamban 2019 yana sukan Manzon Allah (SAW) bayan malamin ya karanto wani Hadisi da Anas Bin Malik (RA) ya ruwaito (Hadithil Hajjah), cewa wata mata ta zo wurin Manzon Allah (SAW) tana neman sa da alfasha, kuma ya biye mata (Wal’iyazu billah).
Lauyoyin Abduljabbar karkashin jagorancin Barista Umar Muhammad sun tambayi Adamu ko ya karanta litattafan da malamin ya kafa hujja da su a hadisan biyu.
Adamu ya amsa musu cewa ya karanta litattafan amma bai ga abin da malamin ya yi ikirari ba a ko’in a cikin littafin Bukhari ko Muslim da malamin ya kafa hujja da su da.
Lauyoyin sun yi masa tambaya game da akidarsa ko mazhabar da yake bi, amma ya ki amsawa.
An kuma tambaye shi ko akwai wani sabani tsakaninsa da Abduljabbar, amma ya ce babu, “Da akwai wani rashin jituwa tsakanina da shi ai ba zan rika halartar karatuttukansa ba.”
– Akwai karin shaidu –
Bayan yi wa shaidan na farko tambayoyi, lauyan gwamnatin ya shaida wa kotun cewa akwai shaida na biyu da zai zai gabatar wa kotun, amma sai a zama na gaba.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola ranar 28 ga watan Oktoba, 2021 domin ci gaba da sauraron shari’ar.