Hukumar zaɓe ta ƙasa INEC ta kammala kare kanta a gaban kotun sauraron ƙararrakin zaɓen jihar Kano ba tare da gabatar da shaida ko ɗaya ba.
Jam’iyyar APC ce dai ta kai karar INEC, Gwamna Abba Kabir Yusuf da jam’iyyarsa ta NNPP bisa rashin amincewa da sakamakon zaɓen da INEC ta sanar.
Sai dai a ranar Alhamis, lauyan INEC Emmanuel Oshayomi ya shaidawa kotu cewa babu wani shaida da zai gabatar.
Kamata ya yi zaben Kano ya zama ‘inconclusive’ – APC
An baza ’yan sanda 18,748 saboda zaben Kano
Ya ce, “mun yi nazarin ƙarar da aka shigar kuma mun fahimci cewa mai ƙara bai kawo hujjar cewa INEC ba ta gabatar da zaɓe bisa tanadin dokar zaɓe ta 2022 ba.”
Don haka ya nemi kotu ta rufe sauraron ƙarar.
A ranar 15 ga Yuli ne dai lauyan APC, Offiong Offiong SAN ya kammala gabatar da hujjojinsa bayan da ya kira shaida 32 gaban kotun.
Kotun ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Oluyemi Akintan-Osadebay ta ɗage zamanta zuwa Juma’a inda ake sa ran lauyan Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf zai fara gabatar da kariyarsa.