Babbar Kotun Jihar Kano ta sallami malamin da ya yi wa gawar Nafiu Hafizu wanka da kuma bayar da bayanan karya domin kare Hafsat Suraj (Chuchu) daga fuskantar hukunci a zargin da ake mata da kisan abokin huldar nata.
Malam Nasidi tare da mijin Hafsat, Dayyabu Abdullahi da Adamu Muhammad suna fuskantar tuhumar boye gaskiya don taimaka mata domin kada ta fuskanci hukuncin kisa.
Sai dai dukkaninsu sun musanta laifukan da ake zargin su da, wadanda suka saba da sashe na 167 na Kundin Pinal Kod.
Alkalin kotun, Mai shari’a Faruk Lawan ya sallami Malam Nasidi inda ya bayyana cewa Sashe na 125 ya ba Kwamishinan Shari’ar iko da dama ya sallami ko ya fasa yin wani kes a duk lokacin da ya ga dama.
- Ba na son zama uban gidan kowa a siyasar Kaduna — El-Rufai
- Zargin Rashawa: APC ta dakatar da Ganduje
Tunda farko masu gabatar da kara karkashin jagorancin Barista Halima Yahuza sun nemi kotun da ta cire sunan wanda ake kara na hudu daga cikin shari’ar sakamakon gyara takardar karar da suka yi.
Haka shi’ ma lauyan wanda ake kara na hudu Barista Rabiu Abdullahi ya nemi kotun da ta sallami wanda yake karewa duba da cewa ba shi da hannu a cikin kes din.
Sai dai lauyoyin wadanda ake kara Barista Haruna Magashi da Barista Fauziyya Yusuf sun yi suka inda suka nemi kotun da ta yi watsi da rokon na lauyan gwamnati.
Idan za a iya tunawa wacce ake kara Hafsat Suraj mazauniyar Unguwa uku a Jihar Kano tana fuskantar zargin kashe Nafiu Hafisu wanda idan ya tabbata hukuncinsa kisa ne, karkashin Sashe na 221 na Pinal Kod.
Mai gabatar da kara kuma lauyan gwamnati, Barista Halima Yahuza Ahmad, ta shaida wa kotun cewa a ranar 21 ga watan Disamba, 2023 Hafsa Suraj ta yi amfani da wuka inda ta caccaka wa marigayin a kirjinsa da wasu sassan jikinsa lamarin da ya yi sanadiyyar rasuwarsa.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Faruk Lawan ya bayar da umarnin tsare wadanda ake zargin a gidan yari.
Haka kuma ya dage sauraren sauraron shari’ar zuwa ranar 6 ga Mayu, 2024 don sake gurfanar da su gaban kotu.