✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shari’ar Atiku da Buhari: Kotu zata sanar da mai nasara

A shari’ar da jam’iyyar adawa ta PDP ta shigar kan kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa da aka yi a babban zaben ranar 23 ga Fabrairu…

A shari’ar da jam’iyyar adawa ta PDP ta shigar kan kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa da aka yi a babban zaben ranar 23 ga Fabrairu 2019, wanda dan takarar shugaban kasa a PDP Atiku Abubakar ya bukaci kotu ta binciki sakamakon zaben Muhammadu Buhari.

Shugaban Kwamitin mutum biyar da aka nada don binciken sakamakon zaben Mohammed Garba, ya ce nan bada dadewa ba za a sanar wa duk jam’iyyun sakamakon binciken da Kwamitin ya yi.

Ba a  sanar da ranar bayyana zartar da hukuncin ba, kamar yadda doka ta tanada amma wa’adin sauraran kararrakin zai zama ranar 14 ga Satumba 2019. Saboda lokacin da aka tanadar don sauraran kararrakin zaben kwanaki 180 ne kawai.