✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sharhin wakar Bakan-Gizo ta Malam Maharazu

Allah cikin ikonSa Ya yi halittu iri daban-daban, wasu ana ganinsu wasu kuma, sun fi karfin mutum ya gansu. Daga cikin wadanda ba a iya…

Allah cikin ikonSa Ya yi halittu iri daban-daban, wasu ana ganinsu wasu kuma, sun fi karfin mutum ya gansu. Daga cikin wadanda ba a iya gani da ido akwai iskokai/aljanu da mala’iku da abubuwan da dan Adam ke amfani da su irin iskar da ake shaka da yunwar da ke damunsa da sauransu. Malam Maharazu Barmu Kwasare ya taskace tarihin wani bakan-gizo da ya yi sanadiyyar mutuwar wadansu mutum shida da suka tarar da shi a cikin rijiya ba tare da sun san yana ciki ba. Al’amarin ya faru a 1396 Bayan Hijira wadda ta yi daidai da  1975 Miladiyya, kuma lokacin Malam Maharazu na da shekara 59 a duniya. Ya sanya wa wakar suna “Wakar Jinni Sago”.  Malam Maharazu ya kira sagon da jinni domin ba a ganinsa. Halittar da ba a gani kuwa, ga Bahaushe ko dai mala’ika ko kuma aljani. Idan aka samu wadanda ba su ba kuma ba a ganinsu, to mai yuwuwa ne suna tare da aljanu.

 

Sago na da sunaye daban-daban da ake kiransa da su. Wannan bambancin sunayen ya jibinci wurare da al’ummar da ke zaune a can. Wadansu mutane na kiransa sago wadansu kuma, bakan-gizo suke kiransa. Akwai masu kiransa zunni wadansu kuma, masha-ruwa suka fi saninsa da shi.

 

A wancan shekara ce jama’ar Unguwar Rungumi da ke cikin garin Sakkwato suka himmatu domin gyara wata tsohuwar rijiya don magance karancin ruwan sha. Duk kokarin da suke yi na hada aikin gayya a gyara rijiyar babu wanda ya san akwai bakan-gizon a cikinta. Da sun sani da ba su shiga ciki ba amma da yake Allah Ya kaddaro musu wannan lamari, babu mahani ga faruwarsa. Domin tabbatar da wurin da abin ya faru, ga abin da Malam Maharazu ya ce:

 

Shiyya ta Rungumi can marina wajen kwalta,

Jabbaru Ya kaddaro musu waki’a har da sago.

 

A lokacin da za a gyara rijiyar mutane sun taru sosai domin gudanar da aikin. Ga al’ada aikin gayya ba a barin mutum daya da aiki ko shi kadai ne gwani sai dai a hada shi da masu taimaka masa domin aiki ya gudana da sauri yadda ake bukata. Ana haka sai wadansu mutum biyar suka shiga rijiyar daya bayan daya. Saukarsu cikin rijiyar ke da wuya sai sagon (aljanin) ya fara cutar da su  ta hanyar sake musu zafin da aka ce yana da shi. Domin tabbatar da haka, ga abin da Malam Maharazu Kwasare ya ce:

 

Sago maciji na kuma aljani dai na,

Sago wuta na zama zafi ga jinni sago.

 

Baitin da aka kawo ya tabbatar da cewa, bakan-gizo aljani ne domin ba a ganinsa balle a san yana wuri. Abin da ke sanya a gane yana wuri kawai shi ne idan aka ga barna irin wadda ya saba yi ta faru da kuma sauran alamomin da ke nuna shi ne kamar tarar da matsanancin zafi a wurin da yake zaune. Akan gane haka domin jama’a sun san kowane abin halitta da aikin da yake yi musamman shi da aka san wurin zamansa ba su zarce rami da kogo da bigar rijiya ba. A kan haka ga abin da Malam Maharazu ya ce:

 

Kogo da rame da biga har kurunguruma,

Ga Rabbana suke har bisa rijiya da sago.

 

Wata alama da ke nuna alamun akwai sago a cikin rijiya ita ce, a ga duk gyaran da ake yi wa rijiyar domin a samu ruwa sai ruwan ya gagara samuwa kuma, ko an samu ba ya wadatarwa har a gaji a fita batunta a yi wata. Duk rijiyar da ke da wannan siffa, ana kyautata zaton akwai masha-ruwa a ciki. Masu aikin gina da gyaran rijiya sun san da haka kuma, mafi yawa daga gare su ake jin wadannan asirrai na rijiyoyin da ba su aminta da su ba saboda wani abu da suka ji ko suka gani ciki lokacin da suka shiga.

 

Dangane da al’amarin da ya faru cikin wannan rijiya Malam Maharazu ya ce mutane na fadar maganganu iri-iri dangane da barnar da masha-ruwan ya yi. Daga cikin maganganun da ake fadi ga abin da Maharazu ya ce:

 

Kila wa kala akwai su kwarai ga annasu,

Komi suka yi bisa kaddara ga sago.

 

Batutuwa ba mu bin su irin na ashararu,

Mu dai tsrin Allah muka so ga jinni sago.

 

Bisa kaddarowar Allah da babu mahani gare ta, sai mutanen biyar da suka shiga rijiyar. Nan take zunnin ya bayyana gare su ya sake musu zafi wanda ba ya da iyaka da ya fi karfin su iya fitowa kai-tsaye. Nan take mutanen suka mutu baki dayansu. A kan haka, ga abin da Malam Maharazu Kwasare ya fada:

 

Mutum biyar Jalla Yay yi kira cikin sa’a,

Guda hukuncin Ilahi Rabban ga sago.

 

Da aka tabbatar da mutuwar mutanen, sai aka shiga shawarar yadda za a fito da su domin yi musu sutura. A cikin kowane lamari akwai wadanda Allah Ya hore wa tambaya ko lakani ko magani ko gwargwado na wasu matsaloli. A nan aka samu wani mutum daya da ya shiga domin ya fito da su. Da tambayarsa da komai da yake shi ma lokacinsa ya yi, ya ci nasarar fitowa da mutane, amma kwana daya ne tskaninsa da su ga kai makabarta kamar yadda Malam Maharazu ya tabbatar da labarin inda ya ce:

 

Na shidda wannan da yaz zo don shi tsamo su,

Wanshekare yab bi su bayan gamo da sago.

 

Bisa bayanin Maharazu ana iya fahimtar cewa, mutum na shida ya ci nasarar fitar da muum biyar daga cikin rijiyar sai dai, shi ma bai tsira ba. Wato bayan ya fitar da su wannan rana aka yi musu jana’iza, shi kuma washegari ya rasu aka yi masa jana’iza kamar yadda aka yi ta wadancan da suka gabace shi da kwana daya. Malam Maharazu ya yi ta’aziyyar mutanen tare da roka musu gafarar Allah kamar haka:

 

Allah Shi gafarta musu don uban Bello,

Shi saukake musu barzahu kan sago.

 

Su san jawabin Nakiri da Munkaran zak kyau,

Fa ba tsawattai balle a ce su buga.

 

Malam ya bayyana cewa, jinni sago ba kamar sauran namun daji yake ba da mutane ke iya korewa daga wurin da yake. Hasali ma, ba a sanin yana wuri sai ya yi aika-aika. A nan, Malam Maharazu na nufin cewa, sago ba irin barewa da damisa ko zaki ko zomo ko kura da sauransu ba ne da ko kuwwa aka yi musu suna iya tashi (gudu) daga wurin da aka gan su su koma wani wuri na daban. Ga abin da Malam Maharazu Kwasare ya fada dangane da haka:

 

Namu na daji ana kuwwa a tashe su,

Ko an yi taro da kuwwa ba a ta da sago.

 

An san cewa ba a ganin aljani ido-da-ido face idan sun rikida zuwa wata siffa ta daban. Ai ko Hausawa cewa suka yi:

 

“Kowa ya ga aljani bai kwana.”

 

Sanadiyyar rasuwar wadannan mutum shida, Malam ya yi addu’o’i daban-daban tare da rokon Allah Ya tayar da sagon ya bar wannan rijiya. Ya roki Allah da surorin Alkur’ani Mai girma da wasu ayoyi da ke cikinsa a wurare da yawa a cikin wakar. Ga misali kamar haka:

 

Albarkacin wa’alamu har duk da ya ayyu,

Albarkacin innamallahu Ka ta da sago.

 

Albarkacin wa’ila Madyana da waman,

Ubarri’u Jalla mun roka Ka ta da sago.

 

Wannan al’amari ne mai girman gaske da tashin hankali da ya faru da ke tabbatar da tarihi a cikin wakokin Malam Maharazu Barmu Kwasare, da fatan Allah Ya sanyaya wa wadannan mutane tare da mu baki daya, amin.

 

Mun samu sharhin wakar Bakan-gizo daga mai lamba

0703 5141 980.