Sunan littafi: For God and Country (Domin Allah Da kasata)Book Title: For God and CountryMarubuci: Chif A.K HorsfallKamfanin Wallafa: LSB PublishingShekarar Wallafa: 2011YawanShafuka: 672Mai Sharhi: Bukar UsmanFarashi: Ba a fada ba
Daga Bukar Usman
Littafin For God and Country (bolume 1), wato Domin Allah Da kasata yana kunshe ne da jawabai da laccoci da falsafar zantuttukan Chif A. K. Horsfall. Littafin an kasa shi zuwa sassa biyar kuma an wallafa shi ne da zimmar kaddamar da bikin cikar marubucin shekarar 70 a duniya. Yana kunshe ne da tarihin rayuwarsa, kamar kuma yadda ya bayyana dalla-dalla yadda ya samu kansa cikin al’amuran mahaifarsa ta Buguma, yankin Neja-Delta. Haka kuma, littafin dai yana dauke da bayanin yadda rayuwar marubucin ta kaya a matsayinsa na Shugaban Hukumar Bunkasa Yankunan Da Ke Samar Da Albarkatun Mai (OMPADEC). Ga duk mai son sanin yadda ta kaya a wannan hukumar, tun daga kafuwarta zuwa karshe, da irin tirka-tirka da sabatta-juyata da suka faru a yayin tafiyar da hukumar zai samu a littafin nan. Haka kuma, mai karatu zai fa’idantu da bayanai dangane da masoyan hukumar da kuma makiyanta na ciki da na waje.
A littafin, akwai gamsassun bayanai da suka shafi al’amuran tsaro, dangantaka tsakanin al’ummar yankin da gwamnati da kuma kamfanonin mai da yankin Neja-Delta. Littafin bai kau da kai ba daga samar da bayanai dangane da siyasar Najeriya, kamar kuma yadda ya bijiro da al’amuran matasa, musamman fadi-tashinsu na rayuwa. Wani abin lura kuma da littafin shi ne, marubucinsa ya tabbatar wa makaranta cewa, dukkan jawabai da laccocin da ke kunshe cikinsa, shi ne da kashin kansa ya rubuta, domin kuwa kamar yadda ya bayyana, bai taba amincewa da shiryayyun jawabai ba daga kowa.
A Kashi Na daya na littafin, wanda aka ware domin bayanan da suka danganci al’amuran siyasa (shafi na 3 zuwa na 163), marubucin ya yi bayanin dalilin da ya sanya ya tafi gudun hijira, bayan ya sauka daga mukamin shugabancin hukumar OMPADEC. “Al’amuran da suka jaza rushe hukumar ta OMPADEC da kuma abubuwan da suka biyo baya, su ne suka sanya na yanke kudurin cewa, babu abin da ya fi alfanu sai in yi kokarin samo maganain matsalolin da aka haddasa a lokacin, shi ne in daraja kaina, in samo hanyoyin sulhu da maslaha, maimakon in bi hanyar jan daga da fito-na-fito da tayar da hargitsi…Wannan dalilin da kuma laulayin dana, su suka sanya na bar kasar a Fabrairu, 1996.” (Shafi na 4). Marubucin dai ya kasance dan gudun hijira na tsawon shekara biyu da rabi. A lokacin da ya dawo gida kuwa, Chif Horsfall, dandazon mutane ne suka tarbe shi da murna, a mahaifarsa, Buguma, Jihar Ribas.
Littafin ya bijiro da al’amuran gwagwarmayar Neja-Delta, inda aka nuna karara cewa, babu abin da al’ummar yankin ke bukata illa “…raba daidai, kyautatawa da adalci ga abin da ya shafi mulki, dukiyar kasa, diyaucin dan kasa da kuma walwalar rayuwa a kasar Najeriya.” Marubucin ya ci gaba, inda ya yi bayani game da hakkin mallakar albarkatun mai dangane da jihohin da ke samar da shi da kuma burin yankin Kudu-Maso-Kudu na ganin ya samar da Shugaban kasa, bukatar da ta kara karfi bayan da aka tabbatar da tsarin yankuna shida a kasar nan a siyasance, lokacin mulkin Janar Sani Abacha.
Al’amuran da suka wakana kuma suka kai ga tsohon Shugaba Goodluck Ebele Jonathan ya samu zama Shugaban kasar Najeriya a 2009, suka kasance wata kaddara da ta zama tamkar biyan bukatar al’ummar Neja-Delta. Marubucin nan ya bayyana haka karara cewa “nasarar da Shugaba Jonathan ya samu a 2011, nasara ce ribi biyu, domin kuwa ta ba su damar darewa madafun iko, kamar kuma yadda ta ba su damar cin gajiyar albarkatun mai da yankinsu ke samarwa, kamar yadda suka dade suna burin samun wannan dama.” (Shafi na 143-149).
Manyan al’amuran da suka danganci hukumar OMPADEC ba su tsaya a Kashi Na daya na littafin ba, sai da suka tsallaka zuwa Kashi Na Biyu (inda aka tattauna Al’amuran Tsaro da Bayanan Sirri, daga shafi na 167 zuwa 245), inda aka zurfafa bayani kan al’amuran da suka shafi tsaro a yankin Neja-Delta da ma Najeriyar gaba daya. Marubucin ya fahimtar da mai karatu yadda aka yi ya zama jami’in tsaro a lokacin da yake dan shekara 17 da kuma yadda ya ci gaba da gudanar da ayyukansa a hukumomin tsaro na kasar nan, har na tsawon shekara 30. Ya ce kwarewar da ya samu a fannin aikin gwamnati, ita ta ba shi damar nakaltar kishin kasa gaba daya, ba kuma tare da yin watsi da muradun al’ummar yankinsa ba. Dalili ke nan ma a duk lokacin da ya tashi gabatar da al’amura da bukatun yankinsa, Chif Horsfall, ba kamar sauran ba, yakan bi ta lalama, amma ba ya kaucewa daga hanyar nema.
Babu shakka, jami’an tsaron Najeriya na yanzu da ma masu zuwa, za su amfana da ilimi mai yawa daga wannan hamshakin jami’in tsaro. Kamar yadda ya bayyana a littafin, marubucin ya taba shirya kuduri ga Majalisar Tarayya, na yadda za a inganta al’amuran tsaron kasar nan. Sai dai bai yi karin bayani a littafin ba, cewa an tattauna kan kudurin a majalisa ko a’a, amma abin lura a nan shi ne, lallai ya kamata wadanda ke da alhakin kula da tsaron kasar nan, ya dace su nazarci wannan kuduri da nufin samun karin dubarar yadda za a inganta tsaron kasar nan. Babi na 20 na littafin nan yana kunshe da dinbin bayanai, inda ya bukaci mutane da suka damu da al’amuran tsaro da su bayyana, wanda haka ke nuna yakinin marubucin cewa “Kula da al’amuran tsaro na kowa ne.” Kamar yadda marubucin ya fada, “Ita hikimar gano sirrin boye ba koyonta ake yi ba, koda kuwa mutum yana da fikira kuma an ba shi horo sosai a kan aikin.” (Shafi na 167).
A Kashi Na Uku, littafin ya yi bayani ne dangane da yadda hukumar OMPADEC ta gudana a lokacinta, (shafi na 249 zuwa 387). A nan an kunsa bayanai masu armashi game da hukumar, sai dai a wannan karon, bayanan suna nuni da yadda aka kafa kwamitoci domin binciko ayyukan da ta gudanar a lokacin da marubucin yake rike da shugabancinta. A yayin da yake gabatar da bayanansa ga kwamitocin da kuma a yayin gabatar da wasu laccoci nasa, marubucin ya yi kokarin bayyana irin matsalolin da ke addabar yankin Neja-Delta. Ya waiwayi baya, inda ya bayyana cewa tun da farko, yankin Neja-Delta yana kunshe da jihohin Akwa Ibom, Bayelsa, Crossriba, Delta, Edo da Ribas a yanzu. Haka kuma, yankin dai a can baya, hade yake da sauran jihohin da ke samar da albarkatun mai, wato Ondo, Abiya da Imo.
Littafin nan kuma ya fahimtar da mai karatu asalin ma yadda aka fara hako mai a Najeriya. Bayani ya gabata cewa kamfanin Shell D’Arcy, a lokacin da yake shirin fara hako mai, ya kafa sansani a Owerri a 1973. Tun da farko, kamfanin ya gano mai ne a Neja-Delta, a Oloibiri (Jihar Bayelsa a yanzu) a 1956, kodayake batun raba kudin shiga, an ce ya faro ne tun a 1946. Tun daga Oloibiri, sai kuma aka gano sannan aka fara hako gurbataccen mai da iskar gas daga sauran sassan Neja-Delta.
Domin ganin magance bukatun kungiyoyin tsirarun kabilun Najeriya, wanda ya hada da na Neja-Delta, Gwamnatin Mulkin Mallaka ta kafa Kwamitin Willink (sunan shugaban kwamitin, Harry Willink, tsohon Shugaban Jami’ar Cambridge) a 1957. An ce Willink ya bayyana yankin Neja-Delta da cewa akwai talauci, don haka ya ba da shawarar a dauke shi a matsayin “yanki na musamman.” Daga bisani kuma a 1960 aka kafa Hukumar Bunkasa Yankin Neja-Delta (NDDB), domin bunkasa yankin.
Bayan NDDB ta kau, an maye gurbinta da wasu hukumomin irinta a shekarun da suka gabata, duk dai da nufin bunkasa yankin. Wadannan hukumomin sun hada da NDRBDA, wacce aka kirkira a 1966. Haka kuma akwai kwamitin da Shugaban kasa ya kafa, mai mazauni a Legas da nufin tallafa wa al’ummomin yankin da ke samar da albarkatun mai. A 1981, an kafa Gidauniya Ta Musamman, domin yankin, wanda Dokar Kudin Shiga ta 1981 ta samar kuma an kafa wani kwamitin a karkashin Minista, a lokacin Gwamnatin Shagari, domin tafiyar da shi. A karkashin mulkin soja na Buhari (1983-1985), an kafa wani kwamitin domin ya tafiyar da gidauniyar, wanda a karkashin Gwamnatin Babangida kuma aka maye gurbinsa da wani kwamitin irinsa. A 1992 kuma aka kafa OMPADEC, wacce ta maye gurbin takwararta ta NDDC da aka samar a 2000. A yayain da ita kuma Ma’aikatar Kula Da Al’amuran Neja-Delta (MNDA), aka kafa ta a 2008.
Za mu kammala