✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Shan maganin maleriya barkatai na iya cutar da mata masu juna biyu – Likita

Likitan ya ce, matan su kare kansu daga shigar kwayoyin cutar maleriya a cikin mahaifarsu.

Wani likitan mai zaman kansa a Benin babban birnin Jihar Edo, Dokta Muhammad Ibrahim Adamu ya shawarci mata masu juna biyu su dage da amfani da gidan sauro idan za su kwanta tare da tsaftace muhalli a koyaushe domin samun kariya daga cutar maleriya.

Likitan wanda ya ba wa mata wannan shawarar a yayin zantawarsa da Aminiya a garin Benin, ya ce, matan su kare kansu daga shigar kwayoyin cutar maleriya a cikin mahaifarsu.

Saboda wannan yakan iya zamewa barazana ga rayuwarsu da kuma abin da suke dauke da shi a cikinsu.

A cewar likitan, “Bincike ya tabbatar da cewa, cutar maleriya takan jawo wa mata masu juna biyu matsaloli da dama a wajen haihuwa ciki har da barin ciki, kuma tana iya rage nauyin jaririn da za a haifa.”

Daga nan sai likitan ya ce, wajibi ne mata masu juna biyu da suke zaune a yankunan da ake samun cutar maleriya su hanzarta neman riga-kafin maleriya a kan lokaci.

Likitan ya kuma gargadi matan da kada su guji shan magungunan maleriya sai sun tuntubi likita ya ba su umarni.

Ya ce, domin shan magani ba tare da an samu shawara daga likita ba, yana tattare da hadari mai muni.

Likitan ya ce, ya kamata tun farko mata masu juna biyu su rika hanzarta zuwa awo domin a san irin maganin da ya dace a ba su.

Saboda ta wannan hanyar ce za a san cutar da take damunsu domin akwai cututtuka masu kama da cutar maleriya.

A karshe likitan ya sake nanata bukatar da ke akwai ta tsaftace muhalli da abinci wanda matan za su ci da kuma ruwan shansu ta yadda ba za su kamu da cutar maleriya da sauransu ba.

%d bloggers like this: