✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shaidan ya kubce

Wani Bafulatani ne ya je aikin Hajji, har sun je wajen jifar Shaidan, ya dauki dutse ke nan zai jifa sai aka bugo masa waya,…

Wani Bafulatani ne ya je aikin Hajji, har sun je wajen jifar Shaidan, ya dauki dutse ke nan zai jifa sai aka bugo masa waya, aka ce ga dansa nan Shaidan ya ribace shi ya aikata ba daidai ba har ’yan sanda sun tafi da shi. Jin haka sai Bafulatani ya ce da karfi: “Kai jama’a, kowa ya yi ta kansa, Shaidan din da muke jifa ya kubce, har ma ya isa Najeriya, yanzu haka ya ingiza dana ya aikata aika-aika!”
Daga Kabir Yahuza Funtuwa (GZG824) 08024133819