Shahararriyar mawakiyar Hausa, Magajiya Dambatta, ta riga mu gidan gaskiya.
Rahotanni daga Jihar Kano sun ce marigayiya Magajiya Dambatta ta rasu ne a ranar Juma’a, bayan jageruwar jinya, tana da shekara 86
Magajiya Dambatta ta kwanta dama ne kimanin shekara uku bayan wani gamgami da aka shirya, wanda ya kai ga saya mata gida da kuma yanka mata albashi.
Gangamin, wanda Editan kafar Daily Nigerian, mai yada labarai ta intanet, Jafar Jafar, ya jagoranta, ya biyo bayan gano mawuyacin halin da mawakiyar, wadda ta yi tashe a shekarun baya, ta tsinci kanta a ciki.
Bayan tsawon lokaci ba tare da jin duriyarta ba, bayan ta samu lalurar makanta, daga bayan aka gano ta tare da ’yar jagora, tana bara, ga kuma tsufa.
Magajiya Dambatta ta yi tashe a shekarun 1970 zuwa 1980.
Masana sun bayyana cewa wakokinta sun yi tasiri a rayuwar Hausawa, musamman wakar ‘Habibu Danmakaranta’, da ta sa aka samu karuwar sanya yara a makaranta a wancan lokaci.