✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Serena Williams ta haifi ’ya mace

Shahararriyar ’yar kwallon tennis ’yar asalin Amurka, Serena Williams a ranar Juma’a 1 ga watan nan da muke ciki ne ta haifi ’ya mace. ’Yar…

Shahararriyar ’yar kwallon tennis ’yar asalin Amurka, Serena Williams a ranar Juma’a 1 ga watan nan da muke ciki ne ta haifi ’ya mace. ’Yar kwallon ce ta sanar da wannan labari da kanta a shafin sadarwarta na yanar gizo.

’Yar kwallon, wacce ta lashe manyan kofuna a gasar tenis daban-daban har sau 23, ba ta shiga gasar tenis ta Wimbledon ta Ingila ta bana ba saboda juna biyun da take da shi.

Tun a watan Afrilun bana ne dai Serena Williams ta sanar da cewa tana dauke da cikin makonni 22 da hakan ya sa aka kiyasta za ta haihu ne a tsakanin karshen watan Agusta zuwa Satumbar wannan shekara.

Cikin ikon Allah hasashen da aka yi ya tabbata inda ta haihu a ranar Juma’ar da ta wuce watau ranar Sallar Layya.

Wannan shi ne karo na farko da ’yar wasan ta taba haihuwa, kuma ita da maigidanta Aledis Ohanian, shi ma dan Amurka sun yi matukar murna game da wannan karuwa da suka samu.

Aledis Ohanian dai yana harkar watsa labarai ne a shafin intanet yana kuma wallafa littatafai kuma an kiyasta kamfaninsa ne na bakwai a Amurka a masu harkar watsa labarai a yanar gizo ta intanet.

Attajirin ya mallaki jarin da ya kai Fam Miliyan 407 kwatankwacin Naira Biliyan 191 da miliyan 697. Ma’auratan sun bayyana farin cikinsu game da wannan karuwa da suka samu, kuma dubban jama’a ne daga sassan duniya suka yi tururuwa wajen aika musu sakonnin taya murna da fatan alheri.