✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saurayi da budurwa sun yi baiko a lokacin gasar

Wani saurayi mai suna Adeboye Osomo, ya samu damar yin baiko tare da budurwarsa Funmilayo Talabi a gaban dubban ’yan kallo a gasar wasanni ta…

Wani saurayi mai suna Adeboye Osomo, ya samu damar yin baiko tare da budurwarsa Funmilayo Talabi a gaban dubban ’yan kallo a gasar wasanni ta kasa da yanzu ke gudana a Abuja.

Adeboye, ya ce ya shafe fiye da shekara 10 yana soyayya da budurwarsa Funmilayo. Ya ce sun fara soyayya ce  a makaranta lokacin da suke sakandare.  Ya yi duk mai yiwuwa don ta amince masa ya aure ta amma ta rika yi masa yawo da hankali.  Ya ce da suka hadu a gasar wasanni ta kasa a Abuja ne ya yi amfani da wannan dama ya durkusa mata a bainar dubban ’yan kallo yana rokon ta amince masa ya aure ta. Ganin haka ne ya sa Funmilayo cikin hawaye ta rungume shi kuma ta mika masa yatsunta inda ya zura mata zoben amincewa ta aure shi (baiko).

Kamar yadda rahoton da kafar watsa labarai ta Naij.com ta kalato ta ce, an yi haka ne a ranar Lahadin da ta wuce a filin wasa na bangaren B a lokacin da ake wasan kwallon raga (Bollyball) a tsakanin jihohin Anambra da Ribas.

Masoyan sun yi farin ciki game da wannan baiko da suka yi kuma suna fatan nan gaba kadan za su sanar da ranar da za a daura musu aure kamar yadda suka shaida wa manema labarai.