✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saura minti 30 su fashe

Wani direba ne a Legas, ’yan sanda suka tsare shi suka ce ya yi laifi, don haka sai ya ba su Naira dubu hamsin ko…

Wani direba ne a Legas, ’yan sanda suka tsare shi suka ce ya yi laifi, don haka sai ya ba su Naira dubu hamsin ko su kai shi Alausa. Ya hada su da Allah su kyale shi suka ce: “Ai mu ba aikin Allah muke yi ba.” Nan da nan sai ya kama dariya, ya dauko wayarsa ya fara magana, yana cewa: “Ranka ya dade, saura minti 30 su fashe, amma bama-bamai 20 ne kawai na dauko, sun ce za su kai motar Alausa, ina nan dawowa da rai yanzu.” Kafin ka ce kwabo, ’yan sandan nan duk sun tsere. Direba ya gama wayarsa ta karya ya wuce da motarsa.
Daga U. S. A. Babawo Yola, 08035038759.