✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saudiyya ta tsare mutumin da ya yi wa Sarauniya Elizabeth II Umarah

Jami'an tsaron kasar Saudiyya sun kama wani da ya yi Umrah ga Sarauniyar Ingila, Elizabeth II

Wani mutum dan kasar Yemen ya shiga komar jami’an tsaron kasar Saudiyya, sakamakon wallafa bidiyonsa na yi wa margayiya Sarauniyar Ingila Elezabeth II aikin Umara.

Mutumin dai ya wallafa bidiyon ne ranar Litinin, inda ya hasko kansa a Masallacin Harami, a bigiren da aka haramtawa wadanda ba musulmi ba sanya kafa.

Cikin bidiyon an gano shi dauke da takardar sanarwar da aka rubuta ‘Sadaukar da Umara ga Sarauniya Elizabeth II, wacce muke rokon Allah Ya sanya ta a Aljannah, cikin tsarkakan bayinSa’.

Bidyon dai da ya karade kafofin sada zumunta a Saudiyyan, inda mutane suka bayyana bacin ransu, tare da yin kira ga hukumomi da su kamo shi.

Gidan talabijin na kasar ya watsa wasu sassan bidiyon da ya janyo ce-ce-ku-cen, sai dai ya disashe takardar sanarwar.

Hukumomin kasar Saudiyya sun haramta yawo da takarduun sanarwa ko wani take a Masallacin Harami tun a kwanakin baya.

Sun bayyana cewa duk da Musulinci ya amince a yi wa wanda ya rasu Umarah, hakan ya takaita ne ga Muslumi kawai, ba irinsu Elizabeth II, wadda Gwamna ce a Cocin Ingila ba.

Yanzu haka dai mutum yana tsare kuma jami`an tsaro sun ce za a dauki matakin shari’a a kansa.