✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saudiyya ta nada mace ta farko a matsayin Jakadiya

Gimbiya Rima bint Bendar ta kasance ’yar kasar Saudiyya mace ta farko da aka fara nadawa a matsayin Jakadiya. Ministan Tsaro kuma Yariman Saudiyya mai…

Gimbiya Rima bint Bendar ta kasance ’yar kasar Saudiyya mace ta farko da aka fara nadawa a matsayin Jakadiya.

Ministan Tsaro kuma Yariman Saudiyya mai jiran gado Muhammad bin Salam ne ya fitar da wata takarda da ta bayar da umarnin nada Gimbiyar a matsayin Jakadiyar Saudiyya a Washington maimakon Halid bin Salman.

Kafar labarai ta TRT ta rawaito daga Kamfanin Dillancin Labaran Saudiyya (SPA) cewa Bin Salman ya bayar da umarnin nada Gimbiyar ce a madadin mahaifinsa Sarki Salman bin Abdülaziz. Gimbiyar Rima bint Bandar bin Sultan bin Abdul’aziz al Saud za ta maye gurbin Yarima Halid bin Salman.

An bayyana cewa Rima wacce za ta kasance mace ta farko da aka taba nadawa a matsayin, mahaifinta Yarima Bender bin Sultan bin Abdul’aziz ya taba zama Jakadan Saudiyya a Washington na tsawon shekara 14.

Halid bin Salman wanda aka cire daga mukami an nada shi mai kula da sojojin Saudiyya a iyakokin Kudancin kasar domin yaki da ’yan  Houthi a kasar Yemen.