✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saudiyya ta kara tsadar kudin motocin haya

A yanzu an rubanya kudin motocin hayar da kashi 16.67 cikin dari.

Hukumar Kula da Sufuri ta kasar Saudiyya ta sanar da kara tsadar kudin motocin haya a biranen kasar da kusan kashi 17 cikin 100.

Sanarwar da Hukumar ta SATGA ta fitar a ranar Lahadi ta bayyana cewa a yanzu Riyal daya shi ne mafi karancin kudin motar haya da za a biya kan kowane sufuri a cikin motar haya mai daukar fasinja hudu.

Dangane da sabon tsarin farashin da hukumar ta fitar, a yanzu za a rika biyan Riyal 2.1 kan karin tafiyar kowace kilomita daya a madadin Riyal 1.8 da aka saba biya a baya.

Jaridar Saudi Gazette ta ruwaito cewa, a yanzu an rubanya kudin motocin hayar da kashi 16.67 cikin dari.

Haka kuma an kara kashi 12.5 cikin 100 kan farashin jiran fasinja duk minti guda, inda a yanzu za a rika biyan Riyal 0.9 maimakon Riyal 0.8 da ake biya a baya.
Za kuma a rika cajin fasinja makamancin wannan kudi idan gudun motar bai haura tafiyar kilomita 20 duk cikin sa’a daya ba.