✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saudiyya ta fitar da tsare-tsaren Aikin Hajjin badi

Rabon hemomin Muna zai kasance bisa tsarin kasar da ta riga kammala biyan kudi.

Hukumomin Kasar Saudiyya sun bayyana tsare-tsaren da aka tanada a shirye-shiryen tunkarar Aikin Hajji na shekara mai zuwa.

Hukumomin sun bayyana cewa daga badi rabon hemomin alhazai a Muna zai kasance bisa tsarin kasar da ta riga kammala shirye-shiryen biyan kudi.

Ministan Ma’aikatar Kula da Aikin Hajji da Umara, Dokta Tawfiq AlRabiah ne ya bayyana hakan a yayin da yake jawabi a taron masu ruwa da tsaki da wakilan ma’aikatun da suka aiwatar da Aikin Hajjin da aka kammala a bana.

Ya bayyana cewa daga Hajjin badi na shekarar 2024, dukkanin hukumomin Aikin Hajji da suka kammala biyan kudinsu su ne za su sami damar zabar wurin da suke so ga alhazansu.

Ministan ya kuma kaddamar da shirin ma’aikatar game da Aikin Hajjin badi na shekarar 2024 inda za su aike da wasika ga kasashen da za su gudanar da aikin Hajjin badi.

Tsarin na Aikin Hajjin badi ya zayyana cewa za a fara shirye-shiryen ne a tsakiyar watan Satumbar wannan shekarar.

Haka kuma, za a soma gudanar da laccoci da bayanai a kan Aikin Hajjin daga a ranar 8 ga watan Janairu, 2024.

Kazalika, Dokta Tawfiq ya ce za a bude bayar da biza daga ranar 1 ga watan Maris 2024 sannan kuma a rufe a ranar 29 ga watan Afrilu 2023.

A cikin sanarwar dai, za a fara jigilar maniyyatan badi daga ranar 9 ga watan Mayun 2024.

Dokta Tawfiq ya jaddada cewa, Masarautar Saudiyya za ta rubanya kokarinta wajen kulawa da jin dadin alhazai inda kuma ya bayyana cewa hakan zai yiwu ne yayin da dukkanin masu ruwa da tsaki suka bayar da bayanai tare da shawarwari game da abubuwan da suke ganin ya kamata a gyara don samun nasarar gudanar da aikin a nan gaba.

Wakiliyarmu ta ruwaito cewa, a yayin taron an bayar da lambar yabo ga kasashen da suka yi rawar gani a Hajjin bana inda kasar Iraki ta yi sauran kasashen zarra.

Sauran kasashen da suka samu nasarar sun hada da Malaysia da Gambiya da Bahrain da Singapor da Afrika ta Kudu da Azerbaijan inda suka sami lambobin yabo a bangarori daban-daban na gudanar da Aikin Hajjin.