✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sau uku mahaifina na yi min ciki —Diyar fasto

Wata mata ta zargi mahaifinta da saduwa da ita har ta dauki ciki sau uku kafin ta yi kaura daga gidansa ta nemi mafaka a…

Wata mata ta zargi mahaifinta da saduwa da ita har ta dauki ciki sau uku kafin ta yi kaura daga gidansa ta nemi mafaka a wajen kungiyoyin kare hakkin mata da yara.

Matar ta ce mahaifin nata wanda fasto ne a cocin CAC, ya fara lalata da ita ne tun a shekarar 2015 a lokacin tana da shekaru 19 a duniya, bayan rasuwar mahaifiyarta.

Kakakin ‘yan sandan jihar Ogun Abimbola Oyeyemi ya ce, “Faston ya amsa laifinsa, ya ce duk abin da yarinyar ta fada gaskiya ne”, kuma za gurfanar da shi bayan kammala bincike.

Matar ta ce baban nata ya yi mata ciki sau uku, yana kuma kai ta wajen wata nas da ke zubar da cikin a duk lokacin da ta dauki ciki.

Ta ce bayan ya zubar mata da cikin a karo na uku ne ta fara yin tsarin hana daukar ciki.

Daga baya ta tsere daga gidan zuwa wajen ‘yan kungiyar kare mata da yara, wadanda suka kai ta wajen ‘yan sanda inda ta shigar da karar mahaifin nata.