✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Satar mota

Wani mutum ne aka sace motarsa, ya je kai rahoto ga ’yan sanda, suka ce ya je za su kira shi in sun gane motar.…

Wani mutum ne aka sace motarsa, ya je kai rahoto ga ’yan sanda, suka ce ya je za su kira shi in sun gane motar. Da ya fita zai tafi ya tarar da wasu ’yan sanda biyu suna tadi, dayan na cewa: “A bara aka yi wannan hanya, wannan ofishinmu ma a bara aka gina shi.” Sai mutumin da aka sace wa mota ya ce: “Ka ji makaryata, a yi abu dazu-dazun nan ku ce bara? Shi ya tsammaci labarin satar motarsa suke yi.

Daga Laminu Umar Abba, 08131364647