✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarrafa Albarkatun Gona: Man Kade (Man kadanya)

A cikin jerin makalun sarrafa albarkatun gona, a wannan makon zan yi bayani a kan yadda dan kasuwa zai yi sodon kwarar kadanya ko kuma…

A cikin jerin makalun sarrafa albarkatun gona, a wannan makon zan yi bayani a kan yadda dan kasuwa zai yi sodon kwarar kadanya ko kuma yadda zai sarrafa kwarar ta kadanya domin samun man da ke cikinta ya yi man kadanya ko man kade (sunan ya danganta daga inda mai karatu ya fito), don sayarwa a kasuwanninmu na gida da kasuwannin kasashen ketare. Zan kuma duba yiwuwar sarrafa shi kansa man kade da dan kasuwa zai saya daga hannun masu yinsa, domin sarrafa shi ya kai shi kasuwannin gida da masana’antun gida da kasuwannin kasashen ketare.
Shi dai man kade ana samunsa ne daga ‘ya’yan itaciyar kadanya, wacce ita kuma ake samu daga kusan dukkanin jihohin Arewa, musamman ma jihohin Arewa maso Yamma da na Arewa maso Gabas. Haka nan kuma ana samun itacen kadanya a jihohin Arewa ta tsakiya da kuma jihohin Kudu da suka makwabce su, irin su Ondo da Oyo da Edo.
Ita itaciyar kadanya da ‘ya’yanta ba baki ba ne ga mazauna karkara a wadannan jihohi. Ana cin ‘ya’yan kadanya a matsayin abun marmari; mai cin kadanya zai cinye tsakar da ke jikin dan kadanya ya yar da kwararsa. A cikin wannan karar ce ake samun kwallon ka\danyar da ake samar da man kade.
Kamar yadda Allah Ya wadata wannan itaciya a cikin kasar nan, haka kuma Ya ba al‘ummae kasar daban-daban basirar sarrafa ta su debi man da ke cikinta domin amfani da shi su biya bukatunsu. Duk dan Najeriya mai kimanin shekara 40, musamman ma wanda ya fito daga jihohin Arewa da na kabilun Yarabawa da ke kudu maso Yammacin kasar nan, ya san man kade a matsayin man fitila da ake saka wa fitilar a- ci-balbal. Haka kuma har yanzu babu wani mai da aka fi amfani da shi wajen magunguna iri-iri a kasar yarabawa kamar man kdde, wanda su ka fi sani da ‘Ori’.
Ana amfani da man kade a nan gida Najeria a matsayin man kwalliya da kare jiki da fuska daga farmakin hunturu. Man na sa fuska da jiki sheki, kuma saboda yana da nauyi, ya kan sa taushin jiki da kuma sa jiki da fuska sheki; kuma ba shi da wani wari mai tozatarwa. Man kuma na mayar da tsohuwa yarinya, inda yake kare fuska daga yakunewa da tattarewa da motsewar tsufa. Sannan kuma man na tausasa busasshiyar fata, ya kuma sa taushin tafin kafa, musamman ma ga mai faso, ya kuma sa fitar kaushin kafa.
A bangaren magani kuwa, mata na yin kitso da shi ko su shafa wa gashi domin maganin amosanin kai, ko kare kai daga amosanin. Man kade kuma na sa gashin kan mata ya yi tsawo ya kuma rika yin sheki. Man kade kuma magani ne kalfiyan wajen warkar da kurarrajin jiki da na fuska da kuma wadanda ake samu da askar aski. Man na kare duwawun jarirai daga kurajen nafkin, inda mata masu goyo kan shafe duwawun jariransu da wannan mai kafin su yi musu kunzugun nafkin.  
    Sauran wurin da ya rage wa wannan fili ba zai isa in karasa lissafa dimbin amfanin da man kade ke yi wa jama’ar kasar nan ba. Wannan ya nuna karbuwar man a kasuwar kasar nan a gargajiyance.
Idan Allah Ya kai mu makon gobe zan duba karbuwar man kade a masana’antun Najeriya da na kasashen duniya da kuma matsayin Najeriya wajen wadata shi a kasuwannin duniya, da kuma yadda dan kasuwa zai sarrafa shi ya fitar da shi ya kuma amfana da shi a wadannan kasuwanni na duniya.