Tsohon Shugaban Kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya ce marigayi sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris ya taimaka masa matuka a lokacin mulkinsa na soja da kuma lokacin da ya sake dawowa a farar hula.
Da yake jawabi yayin addu’ar sadakar ukun sarkin a Zariya, ranar Laraba, Obasanjo ya bayyana shi a matsayin mai son zaman lafiya da sulhu wanda bai taba nuna bambancin kabila, addini ko yanki ba.
- El-Rufa’i ya kira Obasanjo ‘ubangida’ a bainar jama’a
- ‘Yan Najeriya na ji a jikinsu a mulkin Buhari – Obasanjo
Ya ce, “Na zo Zariya ne domin ta’aziyya in kuma yaba wa rayuwar marigayi wanda abokina ne, amini kuma managarcin shawararci.
“Ya zama Sarkin Zazzau kusan a daidai lokacin da na zama shugaban kasa a mulkin soja, lokacin da na dawo kuma a farar hula ya tallafa min sosai.
“Zan iya tuna lokacin da na shiga wata tsaka mai wuya a kan wani rikici a jihar Filato na rasa wanda zai taimaka min, sarkin ne ya neman min mafita.
“Ko mun so ko mun ki, dole wata rana za mu mutu. Marigayi Sarkin Zazzau ya yi rayuwa tagari
“Muna fatan Allah Ya jikan sa Ya kawo zaman lafiya da ci gaba a Masarautar Zazzau, Jihar Kaduna da ma Najeriya baki daya.
Kazalika, taron addu’ar ya samu halarcin gwamnonin jihohi biyar kuma Babban Limamin Masarautar Zazzau, Malam Kasim Dalhatu ne ya jagorance ta.
Gwamnonin da suka halarta sun hada da Kayode Fayemi na Ekiti, Simon Lalong na Filato; Abubakar Bello na Neja; Abubakar Badaru na Jigawa da kuma mai masaukin baki Gwamna Nasir el-Rufai na Kaduna.
A ranar Lahadin da ta gabata sarkin ya riga mu gidan gaskiya bayan shafe shekara 45 a kan karagar mulki.