Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai na shirin gabatar wa Majalisar Dokokin Jihar Kudurin Dokar yi wa tsarin masarautu a jihar gyarar fuska.
El-Rufai yayin gabatar da kasafin kudin 2021 a zauren majalisar ya ce yana aiki domin gabatar wa Majalisar kudurin dokar masarautu da majalisar sarakuna.
“Za mu kawo wa Majalisa karin kudurorin doka domin karfafa shugabanci a jihar
“Hakan zai kawo gyare-gyare a hakimci da sarauta zai kuma kayyade abin da masarautu za su kunsa da rabe-rabensu tare da zamantar da tanade-tanaden masarautu da dokokin da aka gada daga turawan mulkin mallaka”, inji gwamnan.
- Sarkin Zazzau: Gwamnatin Kaduna ta karbi sunaye uku
- Tarihi da rayuwar Sarkin Zazzau Shehu Idris (1937-2020)
Aminya ta gano cewa sabuwar dokar ta El-Rufai za ta kawo sauye-sauye ga tsarin sarauta da kuma hakimci a masarautun jihar.
Bayanin gwamnann na zuwa ne a daidai lokacin da ake rade-radin yana shirin kirkirar karin masarautu biyu daga Masarautar Zazzau.
Ana hasashen gwamnan zai karkasa Masarautar Zazzau ta yanzu zuwa masarautu uku ne gidaje uku da ke kan gaba wajen neman gadar kujerar Sarautar Zazzau su samu dama.
Bisa sabon tsarin da ake hasashe, Masarautar Zazzau za ta koma masarautu uku da suka hada da Zari, Kudan da kuma Kaduna.
Yariman Zazzau ne zai zama Sarkin Zariya, Iya Zazzau zai zama Sarkin Kudan sai kuma Magajin Gari ya zama Sarkin Kaduna.
Tun a ranar 10 ga watan Satumba, 2020 Allah Ya yi wa Sarkin Zazzau na 18, Alhaji Shehu Idris rasuwa bayan shekara 45 yana sarauta.
Tun bayan rasuwarsa ake ta kwan-gaba-kwan baya kan nada sabon sarki tsakanin Masu Zabar Sarki na masarautar da Gwamnatin Jihar.
A makon jiya ne gwamnan ya umarci Masu Zabar Sarkin Zazzau su biyar da su yi watsi da su yi watsi da sunayen masu neman sarautar Zazzau ta 19 da suka mika masa su sake sabo.
Kujerar Sarkin Zazzau ita ce mafi girma a Jihar Kaduna inda kananan hukumomi 11 daga cikin 28 na jihar ke karkashinta.
Kananan Hukumomin da ke karkashin Masarautar Zazzau sun hada da Zaria, Sabon Gari, Giwa, Kudan, Makarfi, Ikara, Kubau, Soba, Igabi, Kaduna ta Arewa da Kaduna ta Kudu.